Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta shiga cikin masu neman Sofyan Amrabat dan kasar Morocco da ke taka leda a kungiyar Fiorentina ta kasar Italiya.
Amrabat ya taka rawar gani a gasar cin kofin Duniya da aka kammala a kasar Qatar a shekarar 2022.
Hakan yasa kungiyoyin Turai da dama suka nuna sha’awar daukar shi a bana.
Daga cikin masu sha’awar daukar dan wasan tsakiyar, akwai Manchester United, Arsenal da kuma Liverpool.