An rantsar da mukaddashin gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar.
An gudanar da rantsuwar ne a dakin taro na Cocoa da ke ofishin gwamna a Akure, babban birnin jihar a ranar Laraba.
- Harin ‘Yan Bindiga: Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato
- An Masa Daurin Rai Da Rai Saboda Yin Fyade A Masallaci A Bauchi
Babban Alkalin kotun jihar, Mai shari’a Olusegun Odusola ya gudanar da rantsuwar da misalin karfe 5:18 na yamma.
Tsohon Gwamna, Oluwarotimi Akeredolu, mai shekaru 67,ya rasu ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba.
Leadership Hausa ta ruwaito cewar ya rasu ne sakamakon cutar sankarar jini.
Gwamnan ya bar mata da ‘ya’ya hudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp