Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Nijeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kakkausar murya da ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) suke yi ko kuma su rufe filayen jiragen saman don nuna goyon bayan su ga kungiyar Malaman jami’o’in.
A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrazaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari ya kawo karshen yajin aikin ba tare da wani jinkiri ba.
ANAP ta Bayyana cewa ci gaba da zaman gidan da daliban manyan makarantu ke yi ya kara haifar da munanan dabi’u a kasar nan, daliban sun fara aikata wasu abubuwa marasa dadi da ka iya lalata makomar rayuwarsu tanan gaba.
ANAP ta yi barazanar cewa za su shiga yajin aikin na hadin gwiwa ta hanyar rufe filayen jiragen sama idan gwamnati ba ta dauki matakan gaggawa ba don magance bukatun ASUU.
Kungiyar ta ce, yajin aikin na sama da watanni hudu ya sa harkar ilimi a Kasar ta zama abin takaici da dariya a gaban duniya.