Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Nijeriya (JUSUN), a Jihar Osun ta dakatar da ayyukanta na masana’antu.
Kungiyar ta shiga yajin aikin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2023, saboda takun saka da suka shiga da babban alkalin jihar, Mai Adepele Ojo.
- Yadda Aka Fara Zaben Fidda Gwani A Amurka
- EFCC Ta Cafke Motoci 21 Makare Da Abincin Da Aka Yi Fasa-kwauri Zuwa Kasashe Makwabta
Sai dai a wata sanarwa a ranar Talata mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar JUSUN na jihar, Gbenga Eludire, ma’aikatan sun sanar da dakatar da yajin aikin.
Eludire, a cikin sanarwar, ya kuma umarci ma’aikatan shari’a a jihar da su koma bakin aiki a ranar Litinin 11 ga watan Maris, 2024.
A wani bangare ya ce: “Bisa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Jihar Osun a karkashin Gwamna Sanata Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, da bangaren shari’a na Jihar Osun karkashin kulawar Hon, Justice O.A. Ojo, Hon. Babban Alkalin Alkalan Jihar Osun da kuma, shugabannin JUSUN karkashin kulawar Kwamared Marwan Mustapha Adamu da Shugaban JUSUN na kasa.
“Sakamakon abubuwan da suka gabata, ina sanar da dakatar da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a ta Nijeriya a Jihar Osun ta fara a ranar 22 ga Nuwamba, 2023, kuma an umarci mambobinmu su koma bakin aiki a ranar Litinin 11 ga watan Maris, 2024.”
Eludire ya jaddada cewa babu wani jami’in shari’a ko dan kungiyar kwadago a jihar da za a ci zarafinsa sakamakon yajin aikin.