Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Nasser Kanaani, ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da alakar diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya.
Haka kuma ta taimaka sosai wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tabbatar da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Nasser Kanaani ya kuma ce, fadada hadin-gwiwa tsakanin kasarsa da Saudiyya, ba dacewa da muradun kasashen biyu kawai ya yi ba, har ma zai amfana ga inganta hadin-gwiwa da mu’amala a wannan yanki, da ma duniya baki daya. (Murtala Zhang)