ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Shugabannin Kasashe Sun Taya Xi Jinping Murnar Ci Gaba Da Kasancewa Shugaban Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
Xi

Shugabannin kasashen duniya na ta mika sakwanni don taya Xi Jinping murnar ci gaba da zama shugaban kasar Sin.

A jiya ne shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin tana ta taka muhimmiyar rawa wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, yayin da take zama abun koyi ga sauran kasashe ta fuskar gyare-gyaren tsarin tattalin arziki.

  • Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Watsi Da Ikirarin Fifita Wasu Al’adu Da Cin Karo Na Wayewar Kai

Ya ce yadda Xi ya ci gaba da zama shugaban kasar ya shaida cewa, al’ummar Sinawa na son ci gaba da bin hanyar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata da kuma bunkasuwa a karkashin jagorancinsa, yana mai cewa, bangaren Zambia na fatan kyautata huldar kud-da-kud a tsakaninsa da Sin.

ADVERTISEMENT

A nasa bangaren kuma, Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana cewa, yadda aka zabi Xi a matsayin shugaban kasar Sin ya shaida imani da amincewa da al’ummar Sinawa ke nuna masa.

Ya ce ana sa ran ganin kasar Sin ta kara samun manyan nasarori a karkashin jagorancinsa. Bugu da kari, shugaba Kagame ya ce ya na son hada kai da Shugaba Xi wajen ciyar da abotar dake tsakanin kasashen biyu zuwa gaba.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Bugu da kari, a cikin sakonsa, babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce, yadda Xi Jinping ya sake zama shugaban kasar Sin ya shaida yadda al’ummar Sinawa suka amince da shugabancinsa da kuma basirarsa ta tafiyar da harkokin kasa.

Ya ce Kawancen kasashen Larabawa na son inganta dangantakar abota tsakanin bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare. (Kande Gao)

Xi
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama
Daga Birnin Sin

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci
Daga Birnin Sin

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia
Labarai

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026
Next Post
Wani Soja Ya Harbe Abokin Aikinsa A Jihar Borno

Wani Soja Ya Harbe Abokin Aikinsa A Jihar Borno

LABARAI MASU NASABA

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?

July 10, 2026
“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Sana’ar Ɗinki: Yadda Telolin Zariya Suka Yi Fice A Sassan Afirka

July 10, 2026
Shugaba Xi Ya Gana Da Firaministan Koriya Ta Arewa A Beijing

Shugaba Xi Ya Gana Da Firaministan Koriya Ta Arewa A Beijing

July 10, 2026
Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.