Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta tabo batun babban taron COP30 a gun taron manema labarai da ma’aikatar ta shirya a yau Litinin, tana mai bayyana cewa, taron ya shaida babbar niyyar sassan kasa da kasa a fannin shawo kan matsalar sauyin yanayi cikin hadin-gwiwa, tare kuma da samar da tabbas ga aiwatar da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya, gami da yarjejeniyar Paris cikin dogon lokaci kuma daga dukkan fannoni a shekaru goma masu zuwa.
Kakakin ta kuma ce, kasarta za ta kara kokari tare da mabambantan bangarori, don aiwatar da nasarorin taron a zahiri, da ingiza hadin-gwiwar sassan kasa da kasa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi, don gina wata kyakkyawar duniyarmu mai tsafta. (Murtala Zhang)














