Ma’aikatar Kasa Da Sufiyo: An Dora Kwarya A Muhallinta A Jihar Katsina?

Duk inda ka ji ance, ma’aikata kasa da sufeyo a kowace jiha a Najeriya, ana nufi wani wuri ne mai mahimmacin a cikin harkokin gwamnati da ke kula sha’anin kasa da sufiyo wanda ya kunshi kula da tsara birane da rarraba filaye da fitar da su domin samar da kyakkyawan muhali.

Sannan idan aka yi sa’ar wanda zai tafiyar da irin wannan ma’aikata cikin kankanin lokaci za a ga cigaba mai ma’ana, saboda haka a wannan jiha ta Katsina za mu duba muga irin yanayin da wannan ma’aikata ta samun kanta a tsawon shekaru, sannan mu duba sabon fasalin da aka yi mata.
Babu shakka kwakwawan shugabanci a kowane irin bangare shi ke zama jagora na kawo cigaba mai ma’ana wanda zai haifar da da mai ido idan aka yi dace da mai kishi da sanin ya kamata domin bunkasar ma’aikata ko kuma su kansu ma’aikatan.
Wannan yana daya daga cikin abubuwa masu matukar mahimmacin da wannan hukuma ko in ce ma’iakata ta rasa tsawon lokaci, wanda hakan ba karamin gibe ya yi wa tafiyar da sha’anin kasa da sufiyo ba a jihar Katsina.
Mahimmacin wannan wuri da kuma irin amfanin da yake yiwa al’umma da kuma gwamnatoci yasa wani lokaci dole sai an rufe ido wajan zaban wanda zai jagoranci hukumar domin a samu bukata ta biya.
Idan kuwa abinda na fada haka yake a tarihi, to ma’aikatar kasa da sufiyo ta jihar Katsina ta dora dan ba na fita daga halin da ta shiga tsawon lokaci, sai dai fa akwai aiki ja a gaban wadanda suka samu kansu a matsayin jagororinta.
Dole sai dan kishin kasa, da mai son cigaba da kawo gyara a sha’anin tafiyar shugabanci ne kadai zai iya daurewa, ya ci je, sannan ya kawo gyara duk da cewa al’amarin ya kazanta.
Wani lokacin sai an shafawa idanu toka kafin samun irin nasarar da ake bukata a cimmawa, domin duk inda ake ce za a yi gyara alamu na nuni da cewa an tafka barna ke nan, saboda haka hakuri dole sai ya yi rana, amma daga karshe za a ga amfanin abin.
Duk idan muka ajiye wannan batun a gefe guda, yanzu muna iya cewa ma’aikatar kasa da sufiyo ta fara dawowa cikin hayyacinta sakamakon sabon angon da ta yi wanda cikin kankanin lokaci aka fara ganin canji mai ma’ana, kuma na alheri, ba irin canjin gwamnatin shugaba Buhari ba.
Duk da kasancewar wannan ma’aikata ta yi wasu shugabanni a baya, kuma sun taka ta so rawar, amma dai idan ana batu na gaskiya, ba a taba yin zabin da ya dace da wannan hukuma ba kamar a irin wannan lokaci da ake bukatar mutane irin su, Alhaji Usman Nadada.
Baya ga kasancewarsa masani a wannan bangare, sannan yana da masaniya a wannan hukuma tun kafin zuwansa, saboda haka lokacin da aka ayyana sunansa a matsayin kwamishinan da gwamna Masari ya zaba duk jama’a sun kai shi wannan ma’aikata tun kafin a tantance shi a rantsar da shi a matsayin kwamishina.
Ko me yasa jama’a suk yi riga malam masallaci? Kila baya wuce sun san Usman Nadada da kokari wajan aikin da ke gabansa, sannan tarihi ya nuna duk inda ya samu kansa, ana ganin fa’idar hakan, saboda haka zamu duba mu ga daga zuwansa dame–dame ya yi a wannan ma’aikata.
Alhaji Usman Nadada ya shaidawa duniya cewa duk da irin matsalar tsaron da jihar Katsina take fama da shi ma’aikatar kasa da sufiyo sune na biyu wajan tarawa gwamnatin kudadan shiga, (wato kudin haraji).
“Idan aka cire hukumar tara kudadan haraji ta jihar Katsina to ma’aikatar kasa da sufiyo ce ke biya da ita wajan tarawa gamwantin jihar Katsina kudadan shiga, domin daga shekarar 2015 zuwa 2020 wannan ma’aikata ta tara fiye da naira miliyan 277” inji shi.
Kazalika ya kara da cewa sun saukaka yadda ake samun takardun shaidar mallakar gida ko fili, inda ya ce yanzu sun maida shi a zamanance wanda cikin sati uku zuwa hudu ana iya samunsa sabanin shekarun baya da ake faman shan wahala kafin a samu wadannan takardu..
“Idan muka duba yadda ake bada takardar shaidar mallakar fili ko gida (certificate of Occuoancy) daga shekarar 1987 lokacin da aka kirkiri jihar Katsina zuwa 2017 takardun shaidar mallaka 4,000 kawai aka iya samarwa ga jama’ar da suka nuna bukata ko suka cancanci samun su. Amma acikin shekaru biyar na gwamna Masari an samar da takardun mallaka 2,000 wannan shima ba karamin nasara ba ce” inji Nadada.
Haka kuma kwamishinan ya yi bayanin cewa gwamnatin ta bayar da manyan filye da aka gina makarantun da masana’antu da kuma gidaje kyauta ga masu saka hannun jari, wanda ya yi bayani wadanda suka amfana da wannan karamcin na gwamnatin Aminu Bello Masari.
Alhaji Nadada yana mai cewa daga cikin wadanda suka amfana da wannan filaye akwai jami’ar sufuri da ake ginawa a garin Daura da kuma kwalejin gwamnatin tarayya ita ma dai a Daura da Barakin Sojoji da na 171 da ke Daura da kuma matsogunnin sojojin sama da ke Katsina da filin gina matatar Mai da ke Mashi.
Da ya juya game da wadanda gwamnati ta biya diyyar wurare kafin ta yanka su ya ce sun biya kudi fiye da naira biliyan daya ga mutane daban-daban a matsayin diyya wanda doka ta bada damar a biya.
Wannan ya nuna irin jajircewarsa wajan ganin jama’a ba su yi kuka da wannan gwamnati ba musamman wajan biyansu hakkukinsu, wanda a baya sai dai muka rika jin ana Allah Ya isa, yanzu haka a Katsina har titin Allah Ya isa ke akwai.
Babu shakka wannan makudan kudade da aka biya a matsayin diyya sa zu taimaka matuka gayya wajan bunkasa tattalin arzikin jihar Katsina tare da samar da cigaba ta fuskoki daban-daban, wannan kadai ya isa ace a wannan karon a dora kwarya a muhalinta.
wani abin birgewa da ya fito daga bakinsa shi ne, inda ya ce nan ba da jimawa ba ma’aikatar kasa da sufiyo zata canza akalar neman mallakar takardun shaidar mallakar fili da gidaje zuwa na’ura mai kwakwalwa ba tare da an sha wata wahala ba.
Saboda a bayanansa ya ce duk wasu manyan al’amuransu sun mayar da su zuwa kwanfuta domin kara saukaka aikinsu na yau da kullun, kuma a na iya cewa ma’aikatar kasa da sufiyo ta jihar Katsina ta zama sahun farko na shiga zamani a dama da ita.
Mutane irin su Alhaji Usman Nadada su ne daman ya kamata a ce suna rika da madafun ikon irin wadannan domin ko ba komi suna kare mutunci wanda ya nada akan wannan mukami saboda kwalliya tana biya kudin sabulu ta wannan bangara.
A wannan gwamnatin ta Aminu Bello Masari an bada tabbacin cewa mutane uku sun kasance abin misali wajan fidda shi kunyar jama’ar da suka zabe shi, wato Alhaji Usman Nadada da kuma Hon. Sani Aliyu danlami, sai kuma MD KASROMA Injiniya Suraj Yazid Abukar.
Bayanan sirri na cewa MD KASROMA ya na da wani ma’aikaci da ke ba shi matsala wajan yin abinda ya kamata wato T.O a ma’aikatarsa abinda takai ga ana zargin cewa kamar T.O ne baya sa ana kyautatawa jama’a da kuma yin abinda ya kamata. Allah Ya sauwake Amin.

Exit mobile version