Ma’ikatar kasuwanci da zuba hannun jari ta tarayya, ta bukaci ma’aikan gwamnati kasar nan da su ci gaba kirkiro da ayyuka na da ban domin a kara ciyar da kasar gaba.
Babban Sakatare na ma’aikatar Ambasada Nura Abba Rimi ya yi wannna kiran a Abuja, yayin bikin mako na abokan huddar cinikayya na 2024 da aka saba gudanarwa a fadin duniya.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Ɗaliban Kwalejin Kimiyya Ta Jega Sun Yi Zanga-Zanga Har Da Ƙone-Ƙone
Rimi a cikin asanarwar da Daraktan yada labarai da hudda da jama’a na ma’aiktar Adebayo Lawrence Thomas ya fitar, ya jaddada mahimmaci a kan gudunmawar da ma’aiktan gwamnati ke da shi wajen kara farfado da tattalin arzikin kasar.
Ya sanar da haka ne, ta bakin Daraktar sashen bunkasa kasuwanci ta ma’aikatar Madam Anietie Umoessien.
Ya ce, taken taron ya nuna irin mahimmanci da ma’aikatan suke da shi wajen cimma bukatar da abokan huddar cinikayya.
A bisa al’ada, ana gudanar da makon ne daga ranar 7 zuwa ranar 11 na kowanne watan Okutobar kowace shekara
Rimi ya yi nuni da cewa, lokaci ya yi da za a girmama tare da karrama ko wanne ma’aikacin gwamnati a kan kokarin da ya yi a fanonin tattalin arzikin gwamnati da ban da ban.
Ita ma a na ta jawabin a gurin taron, babbar jami’a ta kasa Madam Nnenna Akajemeli, ta jaddada mahimacin kara bunkasa karsashen hazaikan da ma’aikatan gwamnati da ke a daukacin ma’aikatu, sassan gwamnati da kuma wadanda ke aiki a hukomomi.
Ta ce, taron ya zo a kan gaba, musamman a karkashin kudurin gwanatin shugaba Bola Tinubu na habaka tattalin arzikin kasar nan.