Aikin hukumar bunkasa noman kwakwa ta Legas ce ta taimaka wajen bunkasa harkar ta yadda za a dinga samar da ita sosai ga kasuwa.
Shugaban hukumar Dapo Olakulehin ya ce jihar ita ce kan gaba wajen samar da kwakwa a kasar nan, inda ya kara da cewa, amma ba a iya wadata kasar da ita saboda karuwar masu sarrafa ta a cikin shekara 10 zuwa 15 da suka wuce.
- Tubabbun ‘Yan Boko Haram Sun Gudanar Da Aikin Tsabtace Muhalli A Maiduguri
- “Korar Fulani A Edo: Ina Ake So Wadanda Aka Haifa A Jihar Shekara 50 Su Koma?”
Olakulehin ya ci gaba da cewa, a shekara uku da suka wuce, lokacin da muka ga alamar karuwar bukatarta, sai muka dinga karfafa wa mutane gwiwa kan su shiga harkar domin samar da ita yadda ake bukata.
A shekara hudu zuwa biyar masu zuwa za a fara ganin tasirin hakan idan bishiyoyin suka fara ‘ya’ya, inda ya ce hukumar bunkasa noman kwakwar ta Legas tana da fili, inda take samar da dashen itaciyar da take raba wa jama’a.
Shugaban ci gaba da cewa, a bara ta raba wa manoma har dashe dubu 200 kyauta, amma duk da haka ba su isa ba, inda ya sanar da cewa, a bana kuwa dashe dubu 80 kawai hukumar ta iya raba wa, wanda wannan na nufin masu sarrafa kwakwar a Nijeriya dole ne su ci gaba da sayo ta daga waje kafin wani lokaci nan gaba.
Shi kuwa wani babban jami’i a Ma’aikatar Masana’antu da kasuwanci da zuba jari ta kasa Kaura Arimiye, cewa ya yi gwamnati ta dauki wannan harka a matsayin wata hanya ta rage yawan marasa aikin yi da kuma rage dogaron da kasar ke yi a kan man fetur domin samun kudi daga kasar waje.
Wata mai kamfanin sarrafa kwakwar, wajen yin abubuwa daban-daban Ebun Feludu, ta ce, tana ganin idan gwamnati na son cim ma bukatar hakan to sai ta bunkasa muhimman abubuwan inganta rayuwa kamar wutar lantarki da tituna da sauransu.
Ta ce Nijeriya ta yi kaurin suna wajen rashin wutar lantarki, haka ma tituna ba su da kyau, inda ta kara da cewa, akwai bukatar gwamnatin ta rage hidima da kudin fitar da kayan zuwa kasuwannin duniya.
Shugabar kungiyar manoma da masu sarrafawa da sayar da kwakwar na kasa Nma Okoroji, ta ce mutane na kara samun wayewa da fahimtar cewa harka ce ta samun kudi.
Nma ta ci gaba da cewa, kwakwa za ta iya kara yawan kudin da Nijeriya ke samu, inda ta bayyana cewa, muna da kyakkyawan yanayi da filin nomanta da kuma manoman, da su yi ta.
Ta ce, muna ma fitar da ita kasashe maimakon mu sayo daga ketare, inda ta kara da cewa, mutane da yawa a Afirka ta Yamma na ci da shan ruwan kwakwa.
Ta kara da cewa , aiki karkashin wani shiri na bunkasa samar da kwakwar a kasar nan, tare da tallafin gwamnati, inda ta sanar da cewa, shirin da a karkashinsa ake kudurin dasa itatuwan kwakwa a fili mai girman hekta 10,000 a yawancin jihohin Nijeriya 36 zuwa shekara ta 2027.
Ta sanar da cewa, sai dai babbar matsalar ita ce ta samun ingantaccen irin kwakwar, inda ta ci gaba da cewa, iri ma fi inganci shi ne na aure wanda aka samar daga, hadin doguwar bishiyar kwakwar ta Afirka ta Yamma da kuma gajeruwa ta yankin Asiya.
Ta bayyana cewa, shekara hudu zuwa biyar, ba kamar gajeruwa ta Asia ba, wadda take fara ‘ya’ya a cikin shekara biyu da rabi zuwa uku, inda ta ce amma kuma ita ta aure kwararru sun samar da ita ne musamman domin noma na kasuwanci.
Shi ma wani da ke a cikin fannin mai suna Abiodun Oyelekan, ya ce yana da kyau a yi amfani da kwakwar ‘yar aure saboda yawan ‘ya’yan da take samarwa a shekara.
Ya sanar da cewa, amma tana da tsada domin duk dashe daya ya kai kusan dala shida wanda hakan ya sa ta fi karfin yawancin kananan manoman da ke a cikin fannin a kasar nan.