A shekarun baya-bayan nan, fannin masana’antun raya layin dogo na kasar Sin na samun ci gaba cikin sauri, kuma ayyukan hadin gwiwa da yawa da ake gudanarwa bisa “shawarar Ziri Daya da Hanya Daya” ko BRI, na ci gaba da tafiya bisa daidaito.
A daya hannun kuma, ma’aunan kasar Sin na gina fannin, wadanda aka wallafa da yarukan waje, sun zamo muhimmin mataki dake taimakawa raya shawarar BRI cikin hadin gwiwa da karko, sun kuma zamo ginshikin ingiza fannin cinikayya tsakanin sassa daban daban.
Alkaluma daga hukumar kididdiga ta kasar Sin sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta fitar da irin wadannan ma’aunai da aka fassara da yarukan waje har 1,767, ciki har da 110 da suka jibanci fannonin gina layukan dogo na jiragen kasa dake zirga-zirga a birane, wato bangaren hada taragon dakon fasinja, da tsara layukan dogo, da kafa turakun lantarki da ake bukata da sauransu, wadanda aka yi amfani da su a wasu kasashen waje, kamar layin dogo na Luanda dake Angola, da na Biot a kasar Chile. Kaza lika, sun taka rawar gani wajen ingiza hadin gwiwar gina sauran ababen more rayuwa karkashin shawarar BRI. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp