A ‘yan shekarun nan an samu dinbin mace-mace a yankin arewacin Nijeriya da suka tayar da hankulan a’umma a bangarori da dama da suka hadd da mace-mace ta hanyar hatsarin kwalekwale, hadarin mota, da kuma uwa ubu mastalar tsaro inda ‘yan bindiga ke kashe a’lumma ba tare da wani shakka ba.
An samu hadurran kwalekwale a jihohin da suka hada da Sakwato, Kebbi, Zamfara, Taraba, Adamawa da jihar Neja, hadurran sun yi sadaiyyar mutuwar mutane da dama.
- Fadar Shugaban Kasa Ta Tabbatar Za A Yi Sauye-sauye A Gwamnatin Tinubu
- Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bikin Cikar Daularsu Shekaru 94 Tare Da Karfafa Alaka Da Nijeriya
Haka kuma rayuka na salwanta a yankin arewa ta sanadiyyar hadurra motoci a kan hanyoyuinmu. Ko a makon da ya gabata an yi wani mummunan hadari a kan hanyar Agaye ta Jihar Neja inda mutum fiye da 30 suka riga mu gidan gaskiya.
A kikiddigar hukumar FRSC ya nuna irin yawan mutanen da ke mutuwa a kan hanyoyinmu saboda rashin kyawun hanyoyin da kuma rashin bin ka’idojin hanya da kuma ganganci daga direbobinmu.
Wani bangare da ke yin sanadiyyar mutuwar mutane a Nijeriya musamman arewacin kasar ya hada da ambaliyar ruwa inda bincike ya nuna cewa, daga watan Yuli zuwa watan Oktoba na shekarar 2012 an rasa rayuka da dama lokacin da kogin Nija da Bnuwai suka cika suka batse inda nan take a ka bayar da rahoton mutune mutum 500 da suka rasa rayuwarsu. A wannan lokacin garuruwa da dama sun samu ibtila’in ambaliyar in jihohi kamar su Adamawa, Taraba, Filato da jihar Benuwai suka sami nasu rabon na asarar rayuka da dukiyoyi a sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu. Bayan lafawar ibtila’in an kididda cewa mutum fiye 363 suka rasu, yayin da mutum sama da 2,100,000 suka rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa a jihohin gaba daya.
Haka kuma a karshen watan Yuli na shekarar 2012, akalla mutum 39 suka mutu a jihar Filato sakamakon ambaliyar da aka samu a jihar.
Haka kuma a tsakiyar watan Agusta, a kididdar da hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ta bayar ya nuna cewa, akalla mutum 333 suka mutu a jihar Filato.
Duk dai sakamakon ambaliyar ruwa, sakamakon sakin ruwa daga dam din Lagdo da ke Cameroon mutane da dama sun rasa rayukansu musamman a Jihar Benuwai.
Haka kuma an bayar da rahon mutuwar akalla mutum 300 a shekarar 2022 a lokacin da aka samu ambaliya a jihar Benuwa da Kogi, yayin da kuma kimanin mutum 100,000 ne suka rasa gidajensu.
Mace-macen da suka fi dimauta ‘yan Najeriya a 2023,Kamar kowacce shekara, mutuwa ba ta bar ‘yan Nijeriya sun zauna kawai ba a 2023, ba tare da ta raba su da wasu shahararrun mutane ba.
A kiddigar da hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ta fitar ya nuna cewa akalla mutane 1,048,312 ambaliyar Ruwa ya shafa a fadin Nijeriya daga watan Afrilu zuwa watan Satumba na shekarar 2024.
Haka kuma an rasa rayuka da dama ta sanadiyya ayyukan ‘yan ta’adda a sassan yankin arewacin Nijeriya, ‘yan ta’adda irinsu Bello Turji suna cin karensu babu babbaka, inda kididdiga ya nuna mutane da dama suka raya rayukansu an kuma raba al’umma da dama daga muhallansu. Wadanda suka bar gidajen su saboda ayyukan ta’addanci suna can suna rabe-rabe a matsayin ‘yan gudun hijira a makarantu da wasu wurare.
Haka kuma mutane da dama sun raya rayukansu a sanadiyyar bam da sojojin nijeriya suka sakarwa masu mauludi a wauyen tudun Biri a jiharb Kaduna. Sojoji sun bayyana cewa sun sake bam din ne a bisa kuskure.