An kama wata mace mai shekara 29, mai suna Chioma Okafor a garin Mowe, da ke karamar hukumar Obafemi Owode ta jihar Ogun.
An kama Okafor tare da wani yaro mai shekara 19 mai suna Nweke Joshua, lokacin da suke yin fashi,” in ji mai Magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi.
- LP, Ta Kori Daraktan Yakin Neman Zaben Obi, Okupe Da Wasu 11 Kan Gaza Biyan Harajin Jam’iyyar
- 2023: Gwamnatinmu Za Ta Farfaɗo Da Harkar ilimi Da Walwalar Malamai – Atiku
Oyeyemi ya ce, sun samu nasarar kama wadanda ake zargin ne sakamakon wani sakon sirri da suka samu.
‘Yansanda sun ce, bayar an sanar da su cewa wadanda ake zargin sun kai hari wani shagon sayar da kayan abinci mallakar Johnson Nwokoro a Safari, sun kwashe dullan kudin da ke shagon.
Lokacin da abin ke faru wa, an yi gaggawar sanar da ‘yansanda, wadanda su kuma suka garzayo, kuma suka samu nasarar kama mutum biyun da ake zargi da aikata wannan laifi. Bayan an kama su, sai aka gane cewa, ashe bindigar da suka zo da ita ta roba ce.
A karshe, kwamishinan ‘yansanda, Lanre Bankole, ya umarci, a mayar da wadanda ake zargin sashin bincike na musamman, somin ci gaba da bincikensu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp