Wato abin da jama’a da yawa suke so su sani game da wannan yanayi na sauyi da takaita zagayawar takardun kudi a Nijeriya shi ne shin a sauran kasashen duniya musamman masu tasowa irin Nijeriya da suka yi wannan tsari, sun ci nasara ko ba su ci ba?
Idan za’a iya tunawa a ranar 22 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata wato 2022, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa bullo da sabbin tsare-tsare akan harkokin kudade ya zama tilas biyo bayan wasu matsalolin da suka dabaibaye tsarin hada-hadar kudi da tsaro a Nijeriya.
Har’ila yau ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2022 babban bankin Nijeriyar ya ayyana cewa za’a fara zagayawa da sabbin kudaden da aka sauya wa fasali na takardun Naira 200 da 500 da 1000, sannan tsofaffin takardun kudin za su daina aiki daga ranar 31 ga watan Janairun wannan shekarar, wanda daga karshe aka tsawaita har zuwa 10 ga watan Fabrairu, inda a yanzu aka bar tsohuwar takardar kudi ta Naira 200 kawai ta ci gaba da zagayawa har zuwa 10 ga Afrilun wannan shekarar.
Babban bankin Nijeriyar ya bayyana cewa tsarin zai kasance mai bayar da ci gaba ga tattalin arziki da kuma sa ran cewa wannan sake fasalin kudin zai rage kudaden jabu, da karfafa tattalin arzikin jama’ar al’ummar Nijeriya.
Bugu da kari kuma shi wannan sabon tsarin na sabbi da kayyade takardun kudi daga zagayawa zai sa mutane da yawa su koma amfani da bankuna inda za’a rage al’amuran sace-sace da ta’addanci saboda ba za a sami kudade da yawa ba da za a yi amfani da su don biyan kudin fansa idan an sace mutane.
Sai dai abin tambaya a nan shi ne, shin wannan tsari na babban bankin Nijeriya haka ya kamata a yi shi a cikin takaitaccen lokaci, kamar yadda da yawa ‘yan Nijeriya suke bayyanawa? Sannan kuma wani karin bayani shi ne, ba wai a Nijeriya kawai ne aka yi irin wannan tsarin ba.
Akwai kasshen duniya kamar Indiya da Benezuela da Zimbabwe har da tarayyar da suka sauya kudadensu, amma kuma abin tambaya shi ne, suma haka suka bayar da takaitaccen lokaci wajen aiwatar da shirin kaco kan dinsa?
Tun farko dai ya kamata a fahimta cewa sake fasalin kudin kasa wani tsari ne mai rikitarwa wanda ya kunshi abubuwa daban-daban kamar kirarsu da fasalin tsaronsu da ra’ayin jama’ar kasashen da uwa uba tattalin arzikin kasar. Yayin da kasashe da dama suka yi nasarar sake fasalin kudinsu, an samu wasu lokuta da manufar ba ta tafi yadda aka tsara ba.
Misali kasar Indiya a cikin shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta ba da sanarwar zazzage wasu manyan takardun kudi a wani yunkuri na hana cin hanci da rashawa da almundahana. Matakin dai ya haifar da rudani, saboda an samu karancin sabbin takardun kudi, lamarin da ya haifar da dogwayen layukan da ake yi a bankuna da kuma tafiyar hawainiya a harkokin tattalin arzikin kasar.
Me ya jawo wa Indiya rashin cin nasarar wannan tsarin nata? A binciken da masana tattalin arziki suka yi, sun gano cewa wadannan abubuwan su ne Ummul haba’isin rashin cin nasarar tsarin sauya takardun kudi.
Rashin tsare-tsare: Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa manufofin sake fasalin kudin Indiya suka gaza shi ne rashin kyakkyawan tsari. Gwamnati ta bullo da tsarin kashe kudi a shekarar 2016 don dakile almundahana da cin hanci da rashawa, amma ba a yi shiri sosai ba, kuma sakamakon ya yi tsanani. Fitar da kashi 86 cikin 100 na kudaden kasar da aka yi a wurare daban-daban ba zato ba tsammani ya haifar da rudani tare da kawo cikas ga tattalin arziki.
Batutuwan aiwatarwa: Wani dalili kuma da ya sa manufofin sake fasalin kudin Indiya ya gaza saboda batutuwan aiwatarwa. Gwamnati ta bullo da sabbin takardun kudi bayan da aka yi amfani da su wajen fitar da kudi, amma an samu matsala wajen bugawa da rarraba wadannan kudade. Haka kuma an samu rahotannin cewa an yi ta yawo da takardun kudi na bogi, wanda ya haifar da karin matsaloli.
Rashin wayar da kan jama’a: Gwamnati ta kasa wayar da kan jama’a sosai game da sauye-sauyen da aka samu na tsarin kudaden da zagayawa. Jama’a da dama, musamman mazauna karkara, ba su san da sabbin takardun kudin ba, don haka ba su iya musanya tsofaffin takardunsu zuwa sababbi ba.
Cin hanci da rashawa: Cin hanci da rashawa wani babban al’amari ne da ya taimaka wajen gazawar manufofin sake fasalin kudin Indiya. An samu rahotannin cewa jami’an bankin na karbar cin hanci don musayar tsofaffin takardun kudi, lamarin da ya janyo karancin sabbin takardun kudi da aka samar.
Rashin isassun ababen more rayuwa: Kayayyakin aikin banki na Indiya ba su shirya don magance hauhawar bukatun sabbin bayanan kudi ba bayan an lalata su. An yi dogwayen layuka a bankuna da na’urorin ATM, wanda hakan ya jawo wa mutane wahala matuka, kamar yadda yanzu a Nijeriya ake fuskanta
Kasar Zimbabwe ma tun a lokacin Shugaba Robert Mugabe a farkon shekarun 2000, Zimbabwe ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya kai ga gwamnati ta bullo da sabon kudin, Dalar Zimbabwe. Duk da haka, sabon kudin ba a tsara shi ba kuma ba a tallafa masa da isassun tanadi ba, wanda ya haifar da ci gaba da hauhawar farashin kayayyaki da kuma watsi da kudin a shekarar 2009. Har yanzu Zimbabwe duk da rasuwar Shugaba Mugabe tana dandana kudarta wajen tattalin arziki a dalilin sauya kudin kasar.
Kasar Benezuela ma a shekarar 2018, ta yi kokarin sake fasalin kudinta ta hanyar cire sifili biyar daga tsohuwar kudin da kuma gabatar da “Bolibar mai mulki.” Duk da haka, matakin bai warware matsalolin tattalin arzikin da ta dade tana fuskanta ba, kuma hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da tashi ba bisa ka’ida ba, wanda ya kai ga darajar kudin ta zama kusan ta fadi warwas, har yanzu ita ma kasar Benezuela tana fama da wannan babbar matsalar ta karayar tattalin arziki.
Tarayyar Turai ma ba’a barta a baya ba domin a 1999 kasashen Turai sun yanke shawarar gabatar da sabuwar takardar kudi ta Yuro, amma sauyin bai kasancewa wasu kasashen na Turai wahala ba saboda su abin ya yi musu dadi. Amma wasu kasashe sun fuskanci hauhawar farashin kayayyaki a lokacin mika mulki, yayin da wasu suka fuskanci turjiya daga jama’a game da karbar sabon kudin.
Anan ya kamata a lura da cewa manufofin sake fasalin kudin za su iya yin nasara, amma suna bukatar tsarawa da aiwatarwa a tsanake, tare da daidaita yanayin tattalin arziki da siyasa. Kamar yanzu abin da yake faruwa a Nijeriya idan mun yi tsai da hanklainmu za mu fahimta cewa kasar Indiya ta sami matsala sosai ta yadda kamata ya yi a ce kasar Nijeriya ta koyi babban darasi daga abin da ya faru a Indiya don kauce wa irin matsalar da har yanzu Indiya take fuskanta game da wancan tsari na sauya fasalin kudade da kuma takaita zagayawarsu.