ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Madubin Sauyin Kudi Daga Wasu Kasashen Duniya Masu Tasowa

by Hussaini Najidda Umar
3 years ago
Sauyin Kudi

Wato abin da jama’a da yawa suke so su sani game da wannan yanayi na sauyi da takaita zagayawar takardun kudi a Nijeriya shi ne shin a sauran kasashen duniya musamman masu tasowa irin Nijeriya da suka yi wannan tsari, sun ci nasara ko ba su ci ba?

Idan za’a iya tunawa a ranar 22 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata wato 2022, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa bullo da sabbin tsare-tsare akan harkokin kudade ya zama tilas biyo bayan wasu matsalolin da suka dabaibaye tsarin hada-hadar kudi da tsaro a Nijeriya.

  • Zama Lafiya Ya Fi Zama Dan Sarki
  • Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dage Zaben Sanatan Enugu Ta Gabas

Har’ila yau ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2022 babban bankin Nijeriyar ya ayyana cewa za’a fara zagayawa da sabbin kudaden da aka sauya wa fasali na takardun Naira 200 da 500 da 1000, sannan tsofaffin takardun kudin za su daina aiki daga ranar 31 ga watan Janairun wannan shekarar, wanda daga karshe aka tsawaita har zuwa 10 ga watan Fabrairu, inda a yanzu aka bar tsohuwar takardar kudi ta Naira 200 kawai ta ci gaba da zagayawa har zuwa 10 ga Afrilun wannan shekarar.

ADVERTISEMENT

Babban bankin Nijeriyar ya bayyana cewa tsarin zai kasance mai bayar da ci gaba ga tattalin arziki da kuma sa ran cewa wannan sake fasalin kudin zai rage kudaden jabu, da karfafa tattalin arzikin jama’ar al’ummar Nijeriya.

Bugu da kari kuma shi wannan sabon tsarin na sabbi da kayyade takardun kudi daga zagayawa zai sa mutane da yawa su koma amfani da bankuna inda za’a rage al’amuran sace-sace da ta’addanci saboda ba za a sami kudade da yawa ba da za a yi amfani da su don biyan kudin fansa idan an sace mutane.

LABARAI MASU NASABA

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira Saboda Dakatar Da Shigo Da Motoci Ta Iyakokinta

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, shin wannan tsari na babban bankin Nijeriya haka ya kamata a yi shi a cikin takaitaccen lokaci, kamar yadda da yawa ‘yan Nijeriya suke bayyanawa? Sannan kuma wani karin bayani shi ne, ba wai a Nijeriya kawai ne aka yi irin wannan tsarin ba.

Akwai kasshen duniya kamar Indiya da Benezuela da Zimbabwe har da tarayyar da suka sauya kudadensu, amma kuma abin tambaya shi ne, suma haka suka bayar da takaitaccen lokaci wajen aiwatar da shirin kaco kan dinsa?

Tun farko dai ya kamata a fahimta cewa sake fasalin kudin kasa wani tsari ne mai rikitarwa wanda ya kunshi abubuwa daban-daban kamar kirarsu da fasalin tsaronsu da ra’ayin jama’ar kasashen da uwa uba tattalin arzikin kasar. Yayin da kasashe da dama suka yi nasarar sake fasalin kudinsu, an samu wasu lokuta da manufar ba ta tafi yadda aka tsara ba.

Misali kasar Indiya a cikin shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta ba da sanarwar zazzage wasu manyan takardun kudi a wani yunkuri na hana cin hanci da rashawa da almundahana. Matakin dai ya haifar da rudani, saboda an samu karancin sabbin takardun kudi, lamarin da ya haifar da dogwayen layukan da ake yi a bankuna da kuma tafiyar hawainiya a harkokin tattalin arzikin kasar.

Me ya jawo wa Indiya rashin cin nasarar wannan tsarin nata? A binciken da masana tattalin arziki suka yi, sun gano cewa wadannan abubuwan su ne Ummul haba’isin rashin cin nasarar tsarin sauya takardun kudi.

Rashin tsare-tsare: Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa manufofin sake fasalin kudin Indiya suka gaza shi ne rashin kyakkyawan tsari. Gwamnati ta bullo da tsarin kashe kudi a shekarar 2016 don dakile almundahana da cin hanci da rashawa, amma ba a yi shiri sosai ba, kuma sakamakon ya yi tsanani. Fitar da kashi 86 cikin 100 na kudaden kasar da aka yi a wurare daban-daban ba zato ba tsammani ya haifar da rudani tare da kawo cikas ga tattalin arziki.

Batutuwan aiwatarwa: Wani dalili kuma da ya sa manufofin sake fasalin kudin Indiya ya gaza saboda batutuwan aiwatarwa. Gwamnati ta bullo da sabbin takardun kudi bayan da aka yi amfani da su wajen fitar da kudi, amma an samu matsala wajen bugawa da rarraba wadannan kudade. Haka kuma an samu rahotannin cewa an yi ta yawo da takardun kudi na bogi, wanda ya haifar da karin matsaloli.

Rashin wayar da kan jama’a: Gwamnati ta kasa wayar da kan jama’a sosai game da sauye-sauyen da aka samu na tsarin kudaden da zagayawa. Jama’a da dama, musamman mazauna karkara, ba su san da sabbin takardun kudin ba, don haka ba su iya musanya tsofaffin takardunsu zuwa sababbi ba.

Cin hanci da rashawa: Cin hanci da rashawa wani babban al’amari ne da ya taimaka wajen gazawar manufofin sake fasalin kudin Indiya. An samu rahotannin cewa jami’an bankin na karbar cin hanci don musayar tsofaffin takardun kudi, lamarin da ya janyo karancin sabbin takardun kudi da aka samar.

Rashin isassun ababen more rayuwa: Kayayyakin aikin banki na Indiya ba su shirya don magance hauhawar bukatun sabbin bayanan kudi ba bayan an lalata su. An yi dogwayen layuka a bankuna da na’urorin ATM, wanda hakan ya jawo wa mutane wahala matuka, kamar yadda yanzu a Nijeriya ake fuskanta

Kasar Zimbabwe  ma tun a lokacin Shugaba Robert Mugabe  a farkon shekarun 2000, Zimbabwe ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya kai ga gwamnati ta bullo da sabon kudin, Dalar Zimbabwe. Duk da haka, sabon kudin ba a tsara shi ba kuma ba a tallafa masa da isassun tanadi ba, wanda ya haifar da ci gaba da hauhawar farashin kayayyaki da kuma watsi da kudin a shekarar 2009. Har yanzu Zimbabwe duk da rasuwar Shugaba Mugabe tana dandana kudarta wajen tattalin arziki a dalilin sauya kudin kasar.

Kasar Benezuela ma a shekarar 2018, ta yi kokarin sake fasalin kudinta ta hanyar cire sifili biyar daga tsohuwar kudin da kuma gabatar da “Bolibar mai mulki.” Duk da haka, matakin bai warware matsalolin tattalin arzikin da ta dade tana fuskanta ba, kuma hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da tashi ba bisa ka’ida ba, wanda ya kai ga darajar kudin ta zama kusan ta fadi warwas, har yanzu ita ma kasar Benezuela tana fama da wannan babbar matsalar ta karayar tattalin arziki.

Tarayyar Turai  ma ba’a barta a baya ba domin a 1999 kasashen Turai sun yanke shawarar gabatar da sabuwar takardar kudi ta Yuro, amma sauyin bai kasancewa wasu kasashen na Turai wahala ba saboda su abin ya yi musu dadi. Amma wasu kasashe sun fuskanci hauhawar farashin kayayyaki a lokacin mika mulki, yayin da wasu suka fuskanci turjiya daga jama’a game da karbar sabon kudin.

Anan ya kamata a lura da cewa manufofin sake fasalin kudin za su iya yin nasara, amma suna bukatar tsarawa da aiwatarwa a tsanake, tare da daidaita yanayin tattalin arziki da siyasa. Kamar yanzu abin da yake  faruwa a Nijeriya idan mun yi tsai da hanklainmu za mu fahimta cewa kasar Indiya ta sami matsala sosai ta yadda kamata ya yi a ce kasar Nijeriya ta koyi babban darasi daga abin da ya faru a Indiya don kauce wa irin matsalar da har yanzu Indiya take fuskanta game da wancan tsari na sauya fasalin kudade da kuma takaita zagayawarsu.

Sauyin Kudi
Hussaini Najidda Umar
+ postsBio
  • Hussaini Najidda Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/hussaini-najidda-umar/
    Tasirin Karancin Kudade Ga Kananan Sana’o’i
  • Hussaini Najidda Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/hussaini-najidda-umar/
    Tasirin Karancin Kudade Ga Kananan Sana’o’i
  • Hussaini Najidda Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/hussaini-najidda-umar/
    ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (II)
  • Hussaini Najidda Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/hussaini-najidda-umar/
    ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (I)

MASU ALAKA

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba
Labaran Kasuwanci

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

June 4, 2026
Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira Saboda Dakatar Da Shigo Da Motoci Ta Iyakokinta
Labaran Kasuwanci

Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira Saboda Dakatar Da Shigo Da Motoci Ta Iyakokinta

May 29, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA
Labaran Kasuwanci

Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

May 21, 2026
Next Post
Zaben 2023: Kwankwaso Ya Lashe Akwatin Mazabar Gidan Sarkin Kano

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Lashe Akwatin Mazabar Gidan Sarkin Kano

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.