An kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su bayan wani artabu tsakanin mafarauta da masu garkuwa da mutane a dajin Chida da ke karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya, Abuja.
Shugaban mafarautan, Adamu Usman, ya bayyana haka a lokacin da yake mika wadanda aka ceto ga shugaban Kuje, Abdullahi Suleiman Sabo, a sakatariyar majalisar a ranar Talata.
- Tinubu Ya Maye Sunan El-Rufai, Ya Aike Wa Majalisa Karin Sunan Ministoci
- MDD Da NSCC Sun Yi Bikin Ranar Tsofaffi Ta Duniya Ta 2023
Daya daga cikin wadanda aka ceto, Adamu Ibrahim Takwa, ya ce an yi garkuwa da shi ne a hanyar Takwa-Kwaku a lokacin da yake dawowa daga cin kasuwa ranar Lahadi.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun dauke shi da abokin aikinsa zuwa wasu tsaunuka da koramai inda suka isa maboyarsu a dajin Chida.
Shugaban Kuje, Sabo, ya ce za su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen ganin an shawo kan matsalar garkuwa da mutane a yankin.
Yayin da ya yaba wa mafarauta bisa kokarin da suka yi na ceto wadanda abin ya shafa.
Sabo, wanda shi kuma ya mika wadanda abin ya shafa ga iyalansu, ya bukace su da su kula da harkokin tsaro, su tabbatar sun kai rahoton wasu abubuwa da faruwa cikin al’ummarsu ga jami’an tsaro.
Leadership Hausa tattaro cewa tun da farko masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 10.