Sarkin Bakan Hausa na Afrika, Alhaji Abashe Garba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta hukunta waɗanda suke da hannu a kisan mafarauta 16 da aka yi a garin Uromi, Jihar Edo.
Alhaji Abashe ya bayyana wannan kisan a matsayin wani mummunan lamari wanda ba shi ne karo na farko ba da ake musguna wa ‘yan arewa a kudancin ƙasar. Ya kuma nemi a tabbatar da adalci domin inganta zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
- Zaben Kananan Hukumomi: A Magance Maimaita Magudi A Jihar Kaduna
- Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Kisan Mafarauta A Jihar Edo
A cikin wannan mummunan lamarin, mafarauta 16 a Jihar Ribas sun fuskanci kisan gilla a lokacin da suka akan hanya, inda ‘yan bijilante suka kashe su a yankin Udune, Uromi.
Alhaji Abashe ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma Sarkin Hausawan Afrika, Abdulkadir Dahiru Koguna, yana addu’a Allah ya musu rahama. Ya ce suna buƙatar gwamnati ta tashi tsaye wajen tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan laifi an kama su kuma an hukunta su bisa ga abin da suka aikata. Har ila yau, ya bayyana cewa amfani da bindiga wajen farauta ba sabon abu bane ga mafarauta, yana mai cewa suna da tsari da shaidar aiki wanda zai tabbatar da cewa suna aiki cikin doka.
Alhaji Abashe ya tabbatar da gudunmawar mafarauta wajen samar da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar, yana mai misalta yadda suka taimaka wajen dakile matsalar garkuwa da mutane a Jihar Bauchi, inda ya ce sun yi nasara a wajen dakile wannan matsala a yankin Ningi da Magama Gumau. Ya kuma nemi gwamnatin tarayya da jihohin kasar su kara musu goyon baya domin inganta gudunmawar da suke bayarwa wajen samar da tsaro a ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp