Akalla magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal takwas aka kama a birnin Jinja na kasar Uganda, sakamakon hada wani gangami na murnar doke Manchester United a wasan hamayya da suka buga a gasar Firimiyar Ingila.
Magoya bayan wadanda ke sanye da rigunan Arsenal na dauke da wani abu da aka siffanta shi a matsayin kofin Firimiyar Ingila.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4 A Bauchi
- NIS Ta Samu Gudunmawar Na’urorin Sadarwa Na Miliyoyin NairoriÂ
‘Yan sanda sun ce mutanen ba su da izinin gudanar da gangamin, kuma yin hakan laifi ne a kasar.
Arsenal ta samu nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United da ci 3-2 a wasan da suka gwabza a ranar Lahadi.
Sakamakon ya bai wa Arsenal damar ci gaba da rike teburin gasar inda ta bai wa Manchester City tazarar maki biyar.
‘Yan sanda sun kama magoya bayan wadanda ke cikin jerin gwanon motoci a ranar Litinin da safe, inda daya daga cikinsu ke rike da kofin da suka hada kudi suka saya a wani shago a kasar.
Magoya bayan Arsenal na cike da karsashi a kakar wasanni ta bana, inda suke sa ran lashe gasar Firimiyar Ingila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp