Umar A Hunkuyi" />

Magoya Bayan Jam’iyyar APC Sun Yi Zanga-zanga A Abuja

Dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC sun yi dafifi a Sakatariyar Jam’iyyar na kasa a ranar Litinin, inda suke yin kira da lallai a kori wakilan kwamitin zartaswa na Jam’iyyar.

Jagoran masu zanga-zangar, Opokwu Ojienyi, ya shaida wa wakilinmu cewa wakilan kwamitin zartaswan Jam’iyyar na yanzun su ne dalilin duk wata koma-bayan da Jam’iyyar ke fuskanta a halin yanzun.”
Ya bayar da misalin ficewar Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo daga cikin Jam’iyyar a matsayin misalin “Mummunan jagoranci da shugabannin jam’iyyar suke nunawa.”
Masu zanga-zangar sun bai wa shugabannin Jam’iyyar wa’adin awanni 48 da ko dai su biya masu bukatunsu ko kuma su shirya ma tunkarar zanga-zanga a kasa bakidaya.

Exit mobile version