Masu zanga-zangar goyon bayan zababben shugaban kasa a jam’iyyar APC sanata Bola Ahmed Tinubu, sun gargadi dan takarar shugaban kasa da yasha kaye a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar LP Peter Obi, kan yunkurinsu na yi wa bangaren shari’a da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC barazana.
Masu zanga-zangar dai, sun mayar da martanin ne kan barazanar da Atiku da Obi suka yi a kwanan baya, bayan sun ki amince wa da sakamakon zaben shugaban kasa, inda har ‘yan takarar biyu, suka gudanar da zanga-zanga a hedikwatar hukumar INEC da ke Abuja.
Sun bayyana hakan ne a yayin wani tattaki na godiya zuwa fadar shugaban kasa.
Masu zanga-zangar wadanda suka hada da kungiyar dalibai ta kasa, NANS da sauran kongiyoyin matasa, sun haifar da cunkuson ababen hawa na dan wucin gadi a yayin tattakin.
A jawabin jagoran gudanar da zanga-zangar, Hon. Smart Edwards ya sanar da cewa, ‘ya’yan APC da Bola Tinubu ba za su lamunci wannan mummunar dabi’a ta magoya bayan Atiku da Obi ba ta yadda suke yiwa bangaren shari’a da hukumar INEC barazana.
Ya ce, idan Atiku da Obi na yin jayayya da sakamakon zaben, sai su je kotu don su kalubalanci sakamakon zaben maimakon su dinga yi wa INEC barazana, suna kokarin tarwatsa zaman lafiya a kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp