Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Aliyu Yaro, matashi mai shekara 19, bisa zargin kashe jaririnsa ɗan kwanaki uku da haihuwa.
Yaro, mazaunin unguwar Kwacham a Mubi ta Arewa, ya amsa laifin kuma ya jagoranci Ƴansanda zuwa wurin da aka binne jaririn.
- Ban Yi Nadamar Yakar PDP A Zaben 2023 Ba – Wike
- Mun Shirya Ƙirkiro Sabbin Masarautu A Adamawa – Fintiri
Rahotanni sun nuna cewa, Yaro ya aikata wannan aika-aikar ne bayan mahaifiyar jaririn, ta nemi ya ɗauki nauyin kulawa da shi. Yaro ya je gidan mahaifiyar jaririn da daddare, ya tura ta tafi nemo ruwa, sannan ya ɗauke jaririn daga baya ya binne shi a yankin Girpata a Mubi.
Kwamishinan Ƴansandan Jihar, CP Morris Dankombo, ya nuna damuwarsa kan wannan lamari, tare da bayar da umarnin miƙa lamarin zuwa Sashen binciken manyan laifuka don ci gaba da bincike da kuma gurfanar da wanda ake zargin gaban Kuliya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp