Hajiya Halima (Baba) Ibrahim, mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ta rasu tana da shekaru 86.
Mahaifiyar Sanata Lawan ta rasu a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, 2023, a gidanta da ke garin Gashua, karamar hukumar Bade a jihar Yobe.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa Sanata Lawan shawara kan harkokin yada labarai, Dakta Ezrel Tabiowo, ta ce za a yi jana’izar Hajiya Halima Ibrahim kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar Lahadi 15 ga watan Oktoba, 2023, a garin Gashua da misalin karfe 11 na safe.
“Bayan haka, za a yi jana’izarta marigayiyar a babban masallacin Gashua, da ke fadar Sarkin.
“Sanata Ahmad Lawan ya yaba da irin yadda ake nuna soyayya da goyon baya kan rasuwar mahaifiyarsa.
“‘Yan uwa suna mika godiya ta musamman ga duk wadanda suka mika gaisuwar ta’aziyya da addu’o’i a wannan lokaci,” a cewar Dakta Tabiowo.