Shafin ADABI shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun marubuta littattafan hausa har ma da masu tasowa domin jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rubutunsu.
A yau ma shafi na tafe da wata bakuwar marubuciyar wato; MARYAM FARUK wacce aka fi sani da UMMU MAHEER inda ta bayyana wa masu karatu batutuwa masu yawan gaske da suka shafi rayuwarta da kuma rubutunta.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- Shugabannin Sin Da UAE Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu AISHA IDRIS ABDULLAHI (ALEESHAT) Kamar haka:
Ya sunan Marubuciyar?
Sunana Maryam Farouk wacce aka fi sani da Ummu-maheer a duniyar rubutu da kasuwanci.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
A takaice dai ni haifaffiyar garin kano ce karamar hukumar Dawakin-kudu, na yi karatuna na firamare a ‘Sheikh Umar Kur’anic Collage’, na yi karamar sakandire a ‘Amrah Modern School’ daga nan na karasa a babbar sakandire a kwalejin kimiyya ta ‘Yammata dage garin Garko. Bayan haka na samu shaidar kammala digiri na daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda na karanci Biology, na yi bautar kasa. A bangaren karatun alkur’ani na yi sauka na kuma karanta litattafai fikhu, hadisi da sauransu. Ina da aure, har da zuri’a.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubuce-rubuce?
Zan iya cewa ni dai kawai na tashi na ganni ina da sha’awar kirkirar labarai, tun ban fi shekaru tara a duniya ba na kan dauki littafi nayi ta rubuta labarai. Kusan littattafaina na makaranta bayansu maimakon zane-zane da yara suka saba to no labarai za a gani. Tun ina yin gajeru har ya kai ina cika littafi 40 leabes guda biyu zuwa uku da labari a haka tun mahaifiyata na daukar abun shirme har ya zama idan na rubuta za ta dauka ta karanta ta ce ya yi dadi. Ita ce ma take adana mun su dan idan na gama ni watsar dasu nake kannena su yaga. Zuwana makarantar kwana kawayena suka sake karfafa mun guiwa akan rubutu har na fara tunanin da zarar na kammala sakandire zan shiga harkar rubutu ka’in da na’in sai dai kuma Allah bai nufa ba na watsar da abin na kama karatu.
Kamar wame bangare ki ka fi mayar da hankali a kai wajen yin rubutu?
Gaskiya ba ni da tsayayyen jigo guda daya da nake rubutu akai, ina tabo kowanne bangare ya danganta da labari da kuma irin sakon da nake son isarwa a ciki kama daga soyayyar, zamantakewar aure da ta yau da kullum da sauransu duka ina tabawa.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara rubutu?
Daga fara rubutu na a Facebook za a yi shekaru bakwai kenan amma zamtowata cikakkiyar marubuciya dai shekaru hudu kenan yanzu.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Kamar yanda na fada na fara rubutu tun ina da kananun shekaru kusan ban ma gama sanin mene ne rubutun ba, duk da dai a lokacin ina yi ne a takarda na ajiye makusantana su karanta, to ko bayan na kaddamar da fara rubutu na a manhajar zamani ta Facebook 2017. Alhamdulillah na samu karbuwar da ban yi zato ba maza da mata sun karbi rubutun sun kuma yi rububinsa sai dai ban yi nisan zango ba na dakata. Kusan zance har sannan din sha’awar rubutun dake tare da ni ta sa na fara sai dai kuma ban shiryawa hakan ba, abin da na dauka kawai ba a sannan ubangiji ya nufa zan yi ba, dan haka sai hidimomin karatu da sauran al’amura suka sha kaina kawai na saki abun duk da irin karbuwar dana samu da yadda mutane suka damu da rubutun tun ana bibiyata da tambayar yaushe zan ci gaba har suka hakura suka bar ni. Alhamdulillah a shekarar 2020 lokacin da ubangiji ya kudurta zan yi na sake komawa na dauko littafina wanda na fara shekaru uku na ajiye na sakoshi daga farko a manhajar Wattpad wanda zan ce shi ne silar dawowata rubutu gadan-gadan duk da shi din ma sai da na kwashe kusan shekaru biyu ina yinsa kafin na kammala na fara littafina na gaba wanda shi ne ya zamto mun bakandamiya ya kuma fitar da sunana har aka san da zamana a duniyar rubtun online.
Kafin ki fara rubutu kin nemi taimakon wani ko wata game da rubutu ko kawai farawa ki ka yi?
Gaskiya bayan mahaifiyata ban nemi shawarar kowa ba a bangaren marubuta ko sauran mutane dan ina dan taba karatu a sannan, amma babu wata marubuciya da nake da kusanci da ita gaskiya da zan nemi shawara ko wani abu a gareta, mahaifiyata ta kawayena wanda su suka ringa karfafani da su kadai nayi shawara.
Wane littafi ki ka fara rubutawa?
Littafin dana fara rubutawa shi ne ‘Rubutacciyar kaddarar (Labarin Hamdah)’. Labarin ya samu karbuwa tun a sanda na fara rubuta shi dan a sanda na fara posting din sa a Whatsapp bayan Facebook da na fara bayan group din mata a lokacin har na maza sai da na bude wanda suke karantawa. Amma dakatawar da nayi ba tare da na kammalashi ba ta dakusar da shi, littafi na biyu dana rubuta WATA KISHIYAR sai ya zama kusan shi ne na farko da dayawan mutane suka sanni da shi. Littafi ne da yayi matukar farin jini gurin makaranta kuma shi ya fitar da ni sai bayan na gama shi sannan na sake dawo da Littafi na na farko wanda a Wattpad na karashi na kawo shi Whatsapp.
Ko akwai wani kalubale da ki ka fuskanta bayan da ki ka fara rubutu?
Gaskiya babu wani kalubale dana fuskanta domin har yanzu mahaifiyata ita ce take sake karfafa ni a kan rubutu, ko a bangaren maigidana ma ban samu kalubale ba gaskiya sun yi mun fatan alkhairi kuma suna kan yi.
Ko za ki iya fadawa masu karatu sunayen Labaran da ki ka rubuta?
Yanzu haka cikakkun labarai dana wallafa Online guda hudu ne. Akwai; 1-RUBUTACCIYAR KADDARAR (LABARIN HAMDAH), 2-WATA KISHIYAR, 3-HALIN KISHI (NADAMAR UMAIMAH), 4-MATAR MUTUM. Wadannan sune cikakku dana kammala, akwai wadanda na fara na saki saboda wasu dalilai da kuma wadanda ke kan hanya.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa