Mahangar Masana A Kan Yadda ‘Ya’yan Manya Ke Fita Kasashen Waje Karatu

Daga Khalid Idris Doya,

Nijeriya a halin yanzu sha’anin ilimi na cikin halin kaka-ni-kayi duk kuwa da kokarin da gwamnatoci suke ta cewa suna yi domin ceto sashin wannan matsalar kuwa musamman a makarantun gwamnati ke fama da koma-baya sakamakon kalubale iri-iri da suka hada da matsalar rashin wadatattun kayan koyo da koyarwaya, rashin biyan malamai yadda ya dace, matsalar tsaro, da halin ko-in-kula daga mahukunta da ‘yan siyasa.

A ‘yan baya-bayan nan masana harkokin ilimi na danganta karuwar matsalar sha’anin ilimi da matsalar tsaron da ke addabar kasar nan, suna masu cewa farmakin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ya sake sanya dalibai fita daga makarantar wanda hakan ya kara lafta matsala kan sashin ilimi ke ciki.

A wannan rahoton musamman da LEADERSHIP HAUSA ta hada, masana sun bayyana hangensu da yadda suke kallon za a tunkari kalubalen da ke addabar harkokin ilimi a halin yanzu. Sai dai a wannan karon, masanan sun maida hankali kan fita kasashen waje da ‘ya’yan manya ke yi zuwa kasashen waje, inda suka bayyana hakan a matsayin illa ga makarantun kasar nan.

A bisa wannan matakin, kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta gano tare da yunkurin daukan matakin hana ‘ya’yan manya tafiya kasashen waje neman ilimi matakin da take kallo zai rage kaifin matsalar tabarbarewar harkokin ilimi a fadin Nijeriya.

A wani taron wuni guda da ASUU ta shirya a Bauchi ta dauki matsayar gabatar da kudurin da zai yi kokarin dakatar da ‘ya’yan manya daga zuwa kasashen waje neman ilimi domin tababtar da an hada karfi da karfe wajen ceto sashin ilimi daga halin kaka-ni-kayi da ke ciki a halin yanzu.

Shugaban kungiyar ASUU ta kasa, Farfesa Bictor Osodoke, ya caccaki shugabanni kan matsalar tsaro da cewa hakan ya samo asali ne sakamakon watsi da suka yi da harkar ilimi gami da nuna halin ko in kula da makarantun gwamnati da suke fadin kasar nan.

A cewarsa, manya ko jiga-jigan kasar nan suna da hannu dumu-dumu a lalacewar sha’anin ilimi a Nijeriya ta yadda suke dauke ‘ya’yansu su kai kasashen waje domin neman ilimi mai inganci tare da watsi da sauran ‘ya’yan talakawa wadanda sune suka fi rinjaye, ya ce wannan abin kunya da kaito ne domin kuwa babu abun da hakan ke jawo wa kasar nan illa koma baya da kuma kara ruguza cigaba musamman na ilimi da sakwarkwacewar makarantu da suke fadin kasar nan.

Shugaban ASUU na kasa, ya kuma bayyana cewar yanzu haka suna kan aiki tukuru domin gabatar da wani kuduri mai taken ‘Bring Back Your Children’ ma’ana ku dawo da ‘ya’yanku daga makarantun kasashen waje zuwa na cikin kasar nan, wanda ya ce kungiyoyin fararen hula, masu zaman kansu, kungiyoyin dalibai da na malamai sune za su hadu domin gabatar da wannan kudurin wa majalisar dokoki ta kasa.

“A yau, shugabannin kasar nan sune ummul-aba-isin rugujewar sashin ilimi a fadin Nijeriya. Sun wofintar da ilimi sun nema wa kawukansu mafita sun kuma bar makarantu da ‘ya’yan talaka a haka ko su samu ilimi ko kar su samu su ba damuwarsu bane.

“Sun haifar da yanayin da su da kansu suka illata da kashe harkokin Iliminmu, sune masu neman makarantu a wasu kasashen su kai ‘ya’yansu domin neman ilimi mai inganci alhali makarantunmu suna cikin mawuyacin hali.

“To tabbas mun dukufa wajen sauya wannan domin kuwa za mu mamaye Majalisar Dokoki ta kasa da kudurin da zai dakile hakan.

“Kawai ‘ya’yansu su yi karatu a makarantun da suke Nijeriya, ko Firamare, Sakandari, makarantun gaba da sakandari ko jami’o’i ko kwalejojin ilimi. Idan wannan kudurin ya fito, za mu tattaro kungiyoyin dalibai, da na malamai da kungiyoyi masu zaman kansu,” ya shaida.

A cewar ASUU muddin aka tabbatar da iyalan manyan kasar nan suna karatu a cikin Nijeriya to tabbas kuwa harkar ilimi zai samu muhimmin kulawar da ta dace da za a kai ga fita daga tabarbarewar da ake ciki a halin yanzu. Yana mai cewa za su nemi goyon bayan hakan domin cimma wannan nasarar inda ya kuma kara da cewa, kudirin tabbas zai taimaka sosai wajen kyautata koyo da koyarwa da kuma samun ilimi mai inganci.

Ya na mai cewa, kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan zai samu raguwar ta hanyar yin aiki tare da juna domin ceto kasar nan daga wannan babban matsalar da ke akwai.

Osodoke, wanda ya ce matsalar tsaro ta sanya wa jama’a da dama rashin aminci da kwanciyar hankali a duk inda suke a fadin Nijeriya, yana mai cewa abokan aikinsu da dama suna fargabar yin tafiye-tafiye domin gudun abin da ka iya zuwa ya dawo na garkuwa da mutane ko fashi da makami da sauransu.

Ya kara da cewa, duk wata kasar da ta wofintar da ilimi to tabbas ta bude fagen matsalar tsaro ne wa kanta da kanta, mana mai cewa sai da ilimi ne ake samun kowane cigaba a cikin kowace al’umma.

Ya ce, “Duk kasar da ta ki maida hankali kan sashin ilimi to ta bude fagen matsalar tsaro, kuma irin hakikanin halin da muke ciki kenan a yanzu a wannan kasar.

“Abokan aikinmu (Malamai) da damansu suna jin tsoron tafiye-tafiye. Mutane da dama suna tsoro da fargabar ziyarar ‘ya’yansu a makarantu a yayin da wasu da daman suke tsoron ma tura ‘ya’yansu makarantu domin neman ilimi don fargabar matsalar tsaro.

“Muna wani marhalar da babu wani da yake jin shi yana cikin tsaro mai inganci walau muna tafiya a kan hanyar titi ko jirgi sama ko kuma a layin dogowa. Dukkaninmu muna sane da a kwana-kwanan nan ‘yan bindiga suka farmako layin dogowa da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.

“Kawai abun da muke nema a yanzu shine a yi aikin hadin gwiwa domin daidaito da lamura da shawo kan matsalolin da suke jibge suna addabarmi,” shaida.

Babbar Matsalar Da Ke Addabar Nijeriya Shine Tabarbarewar Ilimi, Inji ANA

Kan halin da sashin ilimi ke ciki, kungiyar marubuta ta kasa wato ‘Association of Nigerian Authors’ (ANA) ta shaida cewar kulubalen da ke fuskantar harkar ilimi babbar matsala ce wanda akwai gayar bukatar shawo kanta cikin gagggawa.

Shugaban kungiyar ANA reshen birnin tarayya Abuja, Taiwo Akerele, ya shaida wa ‘yan jarida a yayin babban Taron kungiyar tare da bikin cikarta shekara 40 da aka gudanar a Abuja cewa, sama da yada miliyan 13 ne suka bar zuwa makaranta a fadin kasar nan, yana mai cewa sashin ilimi na cikin halin tsaka-mai-wuya.

“Akwai matsaloli sosai a harkar ilimi yayin da yara suke cigaba da barin zuwa makaranta. Kafin ‘yan bindiga masu garkuwa su addibi makarantu, akwai yara miliyan 10 da basu zuwa makaranta, yanzu haka yara miliyan 13 ba su zuwa makaranta Wanda babban matsala ce ga kasar Nan,” inji Akerele.

Ya ce wannan matsala ce da take bukatar daukin gagggawa don haka ne ma suke aiki tare da gwamnatoci domin ganin jama’a sun rungumi ilimin Boko hannu biyu-biyu domin fita daga cikin matsalar ilimi da ake ciki a halin yanzu.

Kan matsalar illimi, LEADERSHIP HAUSA ta tattauna da Malam Ibrahim Ayuba, Malami a Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola inda ya bayyana ra’ayinsa da cewa wannan matakin gabatar da kudurin hana ‘ya’yan manya neman ilimi a kasashen waje abu ne tabbas da zai taimaka Kuma zai ceto sashin ilimi daga durkushawa, sai ma yake cewa lokacin daukan wannan matakin ya ma wuce.

“Tuntunin ya kamata shugabanninmu su yi wannan hangen domin idan muka duba zahiri da hakikanin halin da muke ciki na lalacewar ilimi tabbas za mu gamsu cewa shugabanni da ‘yan siyasa da sauran masu hannu da shuni sune suka lalata harkar, da saninsu suke hakan.

“A tunaninsu idan suka hana dan talaka samun ilimi mai inganci hakan zai toshe masa duk wata dama na zama shugaba ko wani abu a nan gaba, kodayake tabbas sun yi wa sashin illa kuma ilimin dan talaka na cikin gariri. Don haka, a ganina idan aka samu dokar da za ta hana jiga-jigai kai ‘ya’yansu waje karatu tabbas za su bada goyon baya da gudunmawar da za a fargado da harkar ilimi a kasar nan.

“Dan siyasa ko shugaba bai damu da hakin da makarantun gwamnati ke ciki ba. Kuma ko a nan Nijeriya din ma in ka lura Kamar Firamare da sakandari ai manyan basu kai ‘ya’yansu makarantu na gwamnatin sai masu zaman kansu. Wanda hakan ke kara jefa makarantun gwamnati a cikin damuwa. Kuma an gano wannan matsalar tun da jimawa. Don haka daukar wannan matakin neman dokar da za ta hana jiga-jigai kai’ya’yansu makarantu kasashen waje na cikin matakan da za a dauka na fargado da ilimi da makarantun kasar nan daga halin kaka-ni-ka-yi,” Inji shi.

Shi kuma James Ayoba, wani dalibi ne a kwalejin Kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya da ke Bauchi nuna farin cikinsa ya yi da jin wannan batu na kudirin da cewa, “su zo muke gwamutsa da su wajen neman ilimi a makarantunmu, idan da matsaloli iyayensu su tashi tsaye wajen gyarawa don iliminmu ya habaka.

Exit mobile version