Kafin shekara ta 2007, yankin Arewacin Nijeriya ke sahun gaba wajen samun dauwamammen zaman lafiya da wadatar abinci saboda arzikin noma da kiwo wanda yake iya kaiwa ko ina a fadin Nijeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita, baya ga hada-hadar harkokin kasuwanci.
Sai dai daga bisani, yankin ya fara shiga cikin ibtila’in rashin tsaro da koma-bayan tattalin arziki sannan ga ibtila’in ambaliyar ruwa wanda ko a bana sai da abin ya faru a jihohi irin su Jigawa da Kaduna da Kebbi da Kano, da kuma na baya-baya nan na Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiya. Bugu da kari, akwai kuma ibtila’in kifewar kwalekwale daban-daban da suka faru a jihohin Kebbi da Zamfara wanda ta lakume rayuka masu dimbin yawa.
- Jarin Kai Tsaye Na Waje Da Ba Na Kudi Ba Da Sin Ta Zuba A Ketare Cikin Watanni 8 Na Farkon Bana Ya Kai Dala Biliyan 94.09
- Karin Harajin Amurka Ba Zai Dakile Sashen Kere-Keren Kasar Sin Ba
Masana sun bayyana samun yawaitar ibtila’i a jihohin Arewa a matsayin alamun karshen duniya, yayin da wasu suka ce akwai sakacin shugabannin yankin, wasu kuma suka alakanta lamarin da rashin bin dokokin Allah.
LEADERSHIP Hausa ta tattaro ra’ayin malaman addinin Musulunci da na Kirista da masanin falsafa domin jin mene ne musabbabin wadannan ibtila’o’i musamman ganin cewa a arewa ne abubuwan suka fi kamari, kana da kuma hanyoyin samun mafita kan irin wadannan musibu da suka addabi arewar.
Shugaban sashin falsafa na tsangayar fasaha ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dakta Abubakar Zariya Ibrahim ya ce a bangaran falsafa, “Muna hangen lamarin a matsayin kaddara da kuma yardar Allah.
Kaddara shi ne wani abu da Allah ya aiko da shi, to amma ya yarda da abin? Alal misali, idan barawo ya yarda ga Allah ne ya kaddara a yi satan, toh Allah ya yarda a yi? Saboda haka sata kaddara ce, amma Allah bai yarda a yi ta ba.
“A falsafance, yawacin musibun nan a irin wannan suke fadowa, wato kaddara da yardar Allah, saboda Allah ne ya kaddara da su amma bai yarda ba, kamar yadda ya kaddara sata amma bai yarda a yi ta ba.
“Yawancin irin wadannan musibu a irin wannan ma’aunin suke, a takkaice kenan. Yanzu bari mu fara da ibtila’in madatsar Alo da ke Jihar Borno, to ka ga wannan ba bangaren da Allah ya yarda da shi ba ne.
“Idan muka duba A 2015, akwai wani binciken masana irin su Dakta Babagana da Bungus da Kolo da Bello suka yi sun nuna irin hadarin da madatsar ruwan take da shi kuma suka nuna bukatar gaggawa ta kula da take nema na gyara, amma gwamnati ba ta dauki mataki ba.
“A 2022, masana irinsu Dakta Lala da Jibril da Umar da Sadik sun yi bincike kan yadda ake gudanar da mulki da ita kanta madatsar ruwan ta Alo dangane da irin hadarin da take ciki da kuma bukatar gyaran gaggawa, amma dukka gwamnati ba ta yi komai a kai ba.
“Kar ka manta duk da afkuwar wannan abu da za mu kira shi kaddara, gwamnati Borno ta aika da tawaga ta musamman wurin domin su je su gano halin yadda wurin yake ciki. Sai suka fada wa duniya cewa babu wata matsala. Kuma babu abin da zai faru. Ba a yi sati biyu ba, sai ambaliyar ta faru.
“Tun daga shekarar 2020 zuwa 2024, gwamnatin ta fitar da kudi domin a gyara wannan dam din. A irin wannan lokacin ne ma’aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Borno ta ce ta kashe kudi naira biliyan 6.5 wajen aikin ofis, amma ita madatsar ruwan babu komai.
“Abin tambaya a nan, barkewar madatsar ruwar kaddara ce ko ganganci? Saboda mu ba za mu kirashi kaddara ba. Sai dai ganganci saboda wannan ba ibtila’i ne daga Allah ba, wanda za a ce ba a san da zuwansa ba.
“Idan muka dauki barayin daji, wannan makarkashiya ce tun shigowar mulkin soja, wato lokacin Ironsy har zamanin Abdulsalam aka dasa mana wannan matsala.
“A lokacin su Sardauna sun rinka shiga lungu da sako suna gina makarantu da hanyoyi, wanda lokacin Turawa an gina titin jirgin kasa ne kadai. Zaman lafiya shi yake haifar da yaduwar ci gaba. Akwai sakacin gwamnati wajen samun ibtila’i. A lokacin zamanin mulkin Yakubu Gowon, gwamnati ta samu kudi ba karami ba a Nijeriya. A lokacin gwamnati ta ce ba ta san mai za ta yi da kudi ba, baya ga lokacin akwai kauyuka da manyan rugage wadanda ba su da ofishin ‘yansanda, ba su da makaranta da asibitoci ballantana titi da zai kawo su cikin gari, da lokacin an yi musu wadannan abubuwa da yanzu duk irin wannan matsalar ta ‘yan fashin daji da babu su.
“Ka ga rashin ilimi da abinci babu ofishin ‘yansanda da za su nuna musu yadda doka take idan da akwai su da ba a sama wannan matsalar ba.”
“Haka kuma akwai bukatar sai gwamnati ta inganta rayuwar al’umma ta bangarori daban-daban idan aka yi haka za a dan samu sauki.” Kamar yadda ya bayyana.
Shi kuwa a mahangarsa, Malamin addini Musulunci, Sheikh Halliru Maraya da ke Jihar Kaduna, ya bayyana cewa rashin tsoron Allah ne ya haifar da irin jarabobin da suke addabar arewacin kasar nan duba da yadda al’ummar yankin suka yi watsi da dokokin Allah.
Malam Maraya ya ce a yanzu aikata miyagun laifiku karuwa suke, wanda muddin aka ci gaba da haka, to babu shakka an kulla abota da shiga musibu kala-kala.
Ya ce, “Ina mai tabbatar maka da cewa sabon Allah ke jawo musiba, wanda yake shafar wanda ya sani da wanda bai sani ba. Wani lokaci kuma sai ka tarar da mutane suna aikata laifi amma Allah sai ya saukar musu da ni’ima. Shi Allah yakan musu haka ne kafin ya kama su.
“Idan za a ci gaba da sabon Allah, to za a ci gaba da samun musiba iri daban-daban a arewacin kasar nan. Allah ya ce ku ji tsoron musiba saboda idan ta zo za ta shafi azzalumai da mutanan kirki. Saboda haka yawaitar sabon Allah shi ne dalilin shiga ibtila’in da ake samu a kasar nan baki daya.”
Shehin Malamin ya kuma bayyana cewa mafita ita ce a koma ga Allah wajen bin dokokinsa, wanda ta haka ne a za a masu saukin irin wadannan musibun.
“A mahanga ta addinin Musulunci mafita ita ce, tsoron Allah. Allah ya ce duk wanda ya ji tsoro Allah, to zai kawo masa mafita. Wadannan musibu na Arewa mafita shi ne, a ji tsoron Allah a rika aikata abin da Allah ya ce, idan aka yi haka, to kamar yadda ya yi alkawari za a samu mafita.
A nasa bangaren, Shugaban Cocin ‘Christ Ebangelical and Life Intervention Ministry’ da ke Barnawa a Jihar Kaduna, Fasto Yohanna Buru ya ce irin wadanan ibtila’in da ke fuskantar yankin Arewacin Nijeriya alamu ne na karshen duniya, musamman ganin yadda malaman addinai suka zama ‘yan amshin shata, su kuma shugabanin babu tausayi da rashin rikon amanar mabiyansu.
Fasto Buru wanda yana daga cikin fastoci da yake rajin samar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan Arewa, ya ce rashin adalci shi ne ya haifar da rashin tsaro. Ya ce akwai rashin tsoron Allah, inda aka fifita son duniya kan tsoron Allah.
“Mu a arewa babu yunwa saboda babu fari, domin fari shi ke kawo yunwa. ‘Yan Arewa su ne suka haifa wa kansu matsala da musiba. Wadannan musibu da suke samun arewa alamun tashin duniya ne, malamai da shugabanni babu tausayin talakawa a kansu.”
Faston ya ce muddin ana bukatar neman mafita, sai a yi taron yi wa kasa addu’a, wanda za a hada malaman addinai da sarakuna da dattawan arewa da sauran talakawa a yi addu’ar samun mafita.
“Shekara goma sha daya kenan ina kiran a samu hadin kan ‘yan arewa domin magance afkuwar irin wadannan musibu, amma shugabannin na Arewa sun ki su kula hakan.” In ji shi.
Matsalar yawaitar afkuwar ibtila’o’i a arewa musamman a ‘yan shekarun nan dai aba ce da ta addabi galibin al’ummar yankin, don haka ya sa aka yi kokarin shirya tarurruka ciki har da wanda aka gabatar game da sha’anin tsaro a Abuja a kwanan baya. Sai dai rashin aiwatar da kudirorin da aka cimma a aikace na kara dagula lissafin lalubo bakin zaren magance lamarin.