Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ba sun kai hari ofishin ‘yan sanda da ke Eika-Ohizenyi a karamar hukumar Okehi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani jami’in dan sanda mai suna Mista Jibril, wanda aka fi sani da ‘Yellow’.
Wani mazaunin yankun mai suna Mallam Momoh Abubakar, ya tabbatar wa da wakilinmu cewar, ‘yan bindigar sun kai harin da misalin karfe 12:15 ma dare, inda suka jefa wani abu mai fashewa ofishin, lamarin da ya sanya daukacin al’ummar yankin tashi daga bacci.
- Peter Obi Ya Jajantawa Ekweremadu Kan Cafke Shi Da Aka Yi a Burtaniya
- Macizai Da Kunamu Na Barazana Ga Rayukan Mutanen Da Aka Sace A Harin Jirgin Kasa
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun dauki tsawon awa biyu suna sha’aninsu a yankin ba tare da an samu dauki daga jami’an tsaro ba.
Sannan ya ce jami’in dan sanda guda daya da ke aiki a lokacin ya rasa ransa, yayin da kuma suka cinna wa motar aikin ‘yan sandan wuta.
“Ina son amfani da wannan dama don jan hankalin jami’an tsaro da su zage damtse wajen dakile irin wannan hari da aka shafe awa biyu ba tare da kawo dauki ba.
“Harin farko da aka kai ofishin ‘yan sandan ranar Juma’a ne shekaru biyar da suka wuce, wannan ma kuma ranar Juma’a aka yi kuma abun mamaki babu wanda aka cafke da ke da alaka da harin.
“A yanzu dana ke magana da kai, akwai firgici da tashin hankali a zukatan mutane. Muna rokon gwamnati ta kawo dauki saboda wannan yanki ba zai iya jurar hare-haren da ake kawo ba, in ji Abubakar.
A halin da ake ciki an ajiye gawar dan sandan da aka kashe a babban asibitin Obandege.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Edward Ebuka, ya tabbatar da faruwar harin.
Sai dai ya ce wanda suka kai harin ba zasu tsira ba, domin rundunar ‘yan sandan jihar zata bankado inda suka shiga.