‘Yan bindiga sun farmaki wasu mutane a masallaci, inda suka kashe wani mutum sannan suka sace wani dan kasuwa da dansa a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.
Wata majiya ta shaida cewar lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a mahadar Jalo da ke unguwar Saminaka a cikin birnin Jalingo a daidai lokacin da ake sallar magariba.
- Sin Dake Bin Hanyar Samun Bunkasuwa Cikin Lumana Wata Dama Ce Ga Duniya
- Ana Ci Gaba Da Cacar Baki Tsakanin ‘Yan Takara Da Magoya Baya Kan Kalaman Atiku
Majiyar ta kuma bayyana cewa dan kasuwar an ce dalibin makarantar sakandare ne.
Ya ce, “An bayar da rahoton cewa ‘yan bindigar sun kashe mutane da dama, ciki har da dan sanda guda, tare da yin garkuwa da mutane sama da 30 a yankin cikin ‘yan watanni.”
Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tilastawa mazauna yankin yin kaura, inda ya ce suna gudanar da ayyukansu ne daga tsaunukan da ke ratsa kogin Lamurde a karamar hukumar Ardo Kola.
DSP Usman Abdullahi, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Taraba, an kasa jin ta bakinsa kan faruwar lamarin.