Wasu mahara sun kai farmaki kauyen Bari da ke Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano, inda suka sace wani basarake da wata matar aure.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Litinin a yankin.
- Masu Kiraye-Kirayen Kwakwaso Ya Yi Wa Obi Mataimaki Ba ‘Yan Siyasa Bane —Buba Galadima
- Uba Sani Ya Zaɓi Hadiza Balarabe A Matsayin Mataimakiyarsa A Takarar Gwamnan Kaduna
Mutanen da aka sace su ne Shehu Bello Bari (Yariman Bari), sai kuma kanwa ga Dagacin garin na Bari, kuma matar aure mai suna Binta Abdulkadir.
Suleiman Abdulqadir mazaunin yankin, ya shaida wa manema labarai cewa ko kafin wannan harin, an taba sace dan uwan matar auren, kafin daga bisani a sake shi.
“Muna cikin matsananciyar damuwa da wannan harin gaskiya, saboda har yanzu babu wanda ya tuntubi iyalansu.”
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba shi da masaniya a kan harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp