Connect with us

LABARAI

Mahaukata Ke Zagaye Da Shugaba Buhari -Dakta Gumi

Published

on

Wani Malamin Addinin Musulunci mai ra’ayin rikau da ke Kaduna, Shaikh Ahmad Gumi, ya yi wa Shugaba Buhari shagube tare da zargin barin jahilan mashawarta da kuma mutanan da sam ba su da tausayin al’umma a zagaye da shi.

Wannan zargin da Malamin na Musulunci ya yi, ya biyo bayan nu na hoton tsohon gwamnan Jihar Kaduna ne, Ramalan Mukhtar Yero, rike da allon tuhumar da ake yi masa.

Da yake yin bayanan bayan kammala karatun tafsirin da yake yi a Masallacin Sultan Bello, da ke Kaduna, ranar Alhamis, Shaikh Gumi, ya kwatanta mashawartan Shugaba Buharin ne da mahaukata, domin a cewarsa, “sam ba sa tare da mutane.”

“Sun kulle Shugaban kasa, ba wanda zai iya gaya masa gaskiya.

“Gaya mani mai hankalin da ke a tare da shi cikinsu. Ba wanda zai iya gaya masa gaskiya.

Malamin na Musulunci ya ce, babbar hanyar samun nasara ita ce, yafiya, gaskiya, da kuma kiran mutane da su aikata alheri da kuma gudan shawarar jahilai.

“Amma tafarkin da wannan gwamnatin ke tafiya a kansa ya nu na a fili cewa tana bin shawarar jahilai ne.

“Idan mun kyale shi ya kai kasan nan ga halaka, ba shi kadai ne zai halaka ba, dukkan mu ne.

“A kullum mu na gaya wa Buhari gaskiya, amma ba ya sauraro domin sun kulle shi.

“Annabin Allah Ya na yafiya, amma Buhari ba ya yi.

“Annabin Allah ba ya tarayya da jahilai, amma Buhari kullum yana son su, yana kuma tare da jahilan,” in ji shi.

“Kokari muke mu sanya Buhari a kan hanya ta gaskiya,” in ji Shaikh Gumi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: