A yau Laraba, 26 ga watan Maris, ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum.
A lokacin taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da wai “rahoto” na baya-bayan nan da Hukumar Kula da Harkokin Taiwan (MAC) ta gabatar, wanda ya yi ikirarin cewa, bayanan da babban yankin Sin ya fitar cewa, mashigin tekun Taiwan ba hanyar ruwa ba ce ta kasa da kasa, an yi ne da nufin “rikitar da jama’a da kuma nuna adawa da ‘yancin Amurka na kai-komo, inda dan jaridar ya ce shin, “me za ku ce?”.
- Yadda Binciken Kayan Tarihi Ke Zakulo Asalin Magabata Da Wayewar Kansu A Kasar Sin
- Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea
Mai magana da yawun babban yankin Sin, Chen Binhua ya bayyana cewa, kasar Sin daya ce kwallin kwal a duniya, kuma Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Don haka dukkan bangarori biyu na mashigin Taiwan mallakin kasar Sin ne, kana kasar tana da cikakken ‘yanci a kansu, da kuma cikakken ikon mallakar mashigin Taiwan.
Jami’in ya kara da cewa, dokokin ruwa na kasa da kasa ba su amince da wani abu da ake kira da “ruwa na kasa da kasa ba.” Kuma kasar Sin tana mutunta hakkin zirga-zirgar dukkan kasashe a tekun Taiwan bisa tsarin dokokin kasar Sin da na kasa da kasa, ciki har da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan dokar teku ta UNCLOS. Sai dai kuma, tana adawa da haramtattun ayyukan ko wace kasa da ke neman kalubalantar ’yanci da ikon mallaka na kasar Sin, da tsaronta, bisa fakewa da sunan “‘yancin kai-komo.”
Haka nan ya ce, mahukuntan Lai Ching-te, a kokarin ‘wai’ neman ’yancin kai, ta hanyar dogaro da ’yan katsalandan na kasashen waje, sun manta da iyaye da kakanninsu, suna ta kururuwa a bainar kasashen waje, tare da salwantar da muradun kasa ba tare da jin kunya ba. Kazalika, sun kirkiri abin da ake kira “rahoto” domin a yi la’akari da karkatattun ikiraran Amurka, tare da hada kai da ’yan katsalandan na waje a takalar fadarsu, inda jami’in ya karkare da cewa, irin wadannan ayyuka ba komai ba ne illa raini kuma zance ne kawai na banza. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp