Ana kira Madagarscar kasar Vanilla, sakamakon ingancin tsirran Vanilla da ake samarwa a kasar, har ma yawan Vanilla da ake samarwa a kasar da ma fitarwa zuwa ketare ya kai na farko a duniya. Kasar Amurka kuma sakamakon yawan Askirim da ake sayarwa a kasar, ta kasance kasar da take kan gaba a yawan shigowa da Vanilla daga kasar Madagascar. Sai dai munanan matakan haraji da Amurka ta dauka a kan kasa da kasa, ya haifar da cikas ga Madagarscar wajen fitar da Vanilla, matakin da har ya daga farashin Askirim da ake sayarwa a kasar. Daidai kamar yadda wani jami’in diplomasiyya na kasar Madagarscar ya fada, harajin da Amurka ta sanya yana haifar da tasiri ga ‘yan kasuwa da al’umma na kasar Madagarscar, sai dai a sa’i daya, yana kuma tasiri ga masu sayayya na cikin gidan Amurka.
“Munafunci dodo ya kan ci mai shi”. A hakika yadda gwamnatin kasar Amurka ta dauki matakan haraji ba bisa ka’ida ba yana haifar da munanan illoli ga kanta. Ta fannin abinci, bayan matsalar karancin kwai da aka fuskanta a kasar Amurka a farkon bana, a watan Yunin da ya gabata, farashin naman sa ya hau har zuwa wani matsayin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, inda farashin nikakken naman sa ya karu da kusan kaso 12% kwatankwacin makamancin lokacin bara. Ban da haka, ‘yan kasuwar shigar da kayayyaki daga waje na kasar sun yi gargadin cewa, sakamakon matakan haraji da gwamnatin kasar ta dauka, farashin tumatir, da na sauran ‘ya’yan itatuwa da ganyaye ma ka iya karuwa da sauri. Hasali ma dai, matakan haraji na haifar da matsaloli ga tattalin arziki na kasar. Rahoton da kamfanin General Motor na kasar ta fitar game da harkokin kudinta cikin rubu’i na biyu na bana ya nuna cewa, matakan haraji na gwamnatin Amurka ta dauka ya haddasa hasarori kimanin dalar Amurka biliyan 1.1 ga kamfanin, kuma ribar da ya ci ma ya ragu da kaso 35.4%. Sai kuma alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Amurka ta samar a karshen Yuni ya shaida cewa, alkaluman tattalin arziki GDP na kasar cikin rubu’i na farko na bana ya ragu da kaso 0.5% kwatankwacin rubu’in karshe na bara. Har ila yau, kamfanin Fitch Ratings ya rage hasashen da ya yi game da makomar kaso 1/4 na sana’o’in kasar Amurka har ya bayyana ta a matsayin tabarbarewa, bisa dalilin rashin tabbas da ake kara fuskanta da kuma raguwar saurin bunkasar tattalin arzikin kasar.
- Kar Ka Zuga Ƴan Arewa Kan Tinubu — Nabena Ya Gargaɗi Kwankwaso
- Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
A akasin haka, wani rahoton da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar kwanan nan game da tattalin arzikin kasar Sin cikin farkon rabin shekarar bana, ya nuna cewa, alkaluman tattalin arzikin GDP ya karu da 5.3% a kasar Sin. Wannan ba karamar nasara ba, musamman a yayin da kariyar ciniki ke addabar duniya tare da haifar da cikas ga farfadowar tattalin arzki, wanda ya shaida ingancin tattalin arzikin kasar Sin, tare da sake tabbatar da al’ummar duniya cewa, bude kofa yana samar da ci gaba, yayin da rufe kofa kan haifar da koma baya. A hakika, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, saurin bunkasar kasar ta fannonin tattalin arziki da zaman al’umma ya tabbata ne sakamakon yadda kasar ke bude kofarta ga ketare, da ma aiwatar da hadin gwiwar cin moriyar juna da kasa da kasa. A sa’i daya kuma, babbar kasuwar kasar Sin, da fasahohin zamani da cikakken tsarin masana’antu na kasar su ma sun samar da alfanu ga kasa da kasa. Duba da cewa, a cikin ‘yan shekarun baya, kasar ta samar da gudummawar da ta kai kimanin kaso 30% na bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya, lamarin da ya sa ta zama babban ginshikin bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Ko da yake har yanzu Amurka tana kare aniyarta ta sanya harajin da bai dace ba kan kasa da kasa, amma ko kadan kasar Sin ba za ta tsayar da bude kofarta da hadin gwiwa da sauran kasashe ba. A satin da ya wuce, kasar ta samu babban ci gaba wajen gina tashar ciniki marar shinge ta Hainan, inda ta sanar da cewa, za a fara aiwatar da tsarin aikin kwastam mai zaman kansa a duk fadin tsibirin Hainan tun daga ranar 18 ga watan Disamban bana. Wato ya zuwa lokacin, za a fadada nau’o’in hajojin da ake cire musu harajin kwastan daga 1900 na yanzu har zuwa 6600, adadin da ya kai kimanin kaso 74% na gaba dayan hajoji.
Amurka tana daukar munanan matakan haraji ne don neman cimma burinta na “mai da Amurka a gaba da komai”, mataki mai son kai ne wanda ba kawai ya lalata moriyar sauran kasashe, har ma da ita kanta. Kasar Sin a nata bangare, tana dukufa a kan bude kofarta ga ketare, don kowa ya ci moriya.
Jama’a, shin mene ne ra’ayinku?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp