Da alamun kasashen da suke ikirarin kare hakkin bil-Adama, su ne kuma suke take wannan hakki ta hanyar kashe fararen hula, wadanda ba su san hawa ba balle sauka. Wai mai dokar barci ya bige da gyangyadi.
Sanin kowa ne cewa, a kan tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa wasu kasashe dake fama da rikici ko tashe-tashen hankula ne, domin su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin wadannan kasashe, amma sabanin haka, sai irin wadannan kasashe, har ma gasar kashe fararen hula suka yi a kasar Afghanistan.
Wani binciken da kafar yada labaran BBC ta gudanar kan shaidun da suka hada da rahotannin sojojin Birtaniyya, da sakonnin imel, da hotunan ramukan harsashi a wurin, ya nuna cewa, wasu mambobin tsohon rukunin mai ba da hidima ga soja na musamman na Birtaniya dake Afghanistan, sun sha kashe fursunoni da fararen hula da ba sa dauke da makamai, har ma su kan yi gasar kisan mutane, daga cikinsu, akwai yiwuwar wata runduna ta kashe mutane har 54 ba bisa kai’da ba, a wa’adinsu na watanni 6 a wurin.
Bayan fallasa wadannan laifuffuka, ma’aikatar tsaron Burtaniya, ba wai kawai ta ki neman afuwa, ko daukar alhakin kai harin ba, amma sai ta yi kokarin yin rufa-rufa, tana mai zargin rahoton na BBC da cewa wai “labarai ne da ba su dace ba kuma wai ba daidai ba ne”. Wannan shi ne kora kunya da hauka.
Hasali ma, ba sojojin Birtaniya ne kawai suka kashe fararen hula babu gaira babu dalili ba. A watan Disamba na shekarar 2020, ma’aikatar tsaron kasar Austriliya, ta fitar da rahoton bincike game da kyamar bil-Adama da sojojinta suka yiwa fararen hula a kasar Afghanistan.
A bangaren Amurka, wadda ke zama kanwa uwar gani, mamayar da aka yi a kasar Afghanistan na tsawon shekaru 20, ta yi sanadiyar rayukan ’yan kasar dubu 174, ciki har da fararen hula dubu 30. Wadannan kasashe su ne suke ikirari kare hakkin Bil Adama a ko da yaushe, to yaya za su bayyana kisan gillar da suke yiwa mutanen da ba su san hawa ba balle sauka a kasashen waje?Duniya na bukatar amsa daga gare su.
Sanin kowa ne cewa, yarjejeniyar Geneva ta bayyana karara cewa, ba daidai ba ne kisa, ko tilastawa, ko musgunawa da ma korar wadanda ke zaune lafiya, yin hakan ta ce haramun ne a lokacin yaki, kuma wadanda ba su taka rawa a yakin ba, za a mutunta su a kowane hali.
Kasashen Amurka da Birtaniya da Austriliya, dukkansu sun sa hannu kan wannan yarjejeniya, amma kuma sun rufe idanunsu, suka kuma rika keta dokokin kasa da kasa, da ma harkokinsu da suka shafi dan-Adam.
Baya ga yadda suke kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba. Laifukan da suke aikatawa, laifi ne ga daukacin bil-Adam, don haka sun cancanci a yi musu adalci. Dole ne kasashen duniya su yi adalci ga wadanda ba su ji ba su gani ba. Domin babu ran da ya fi wani. (Ibrahim Yaya)