Mai gadin kabarin Manzon Allah SAW, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, Allah yayi masa rasuwa a yau Laraba.
Agha Habeeb Muhammad Al-Afari ya jima yana fama da jinya.
Ya yi aiki a matsayin babban mai kula da kabarin Annabi Muhammad SAW, tsawon Shekaru sama da 40.
Za’ayi jana’izarsa bayan Magriba a Masallacin Annabi SAW dake Madina, 13 ga watan Yuli, 2022.
Dakin da aka bizne Annabi Muhammad SAW ana kiransa dakin alfarma ko Rawdah Mubarak, kuma wurin ne aka bizne kalifofin Annabi Muhammad SAW na farko da na biyu, Sayyidina Abubakar (RA) da Sayyidina Umar (RA).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp