Mai Kama Da Messi Ya Musanta Zargin Lalata Da Mata

Reza Paratesh dan kasar Iran da ke da matsananciyar kama da kaftin din Barcelona Lionel Messi, ya musanta yaudarar mata 23 a kasarsa wajen kwana da su, ta hanyar shara musu karyar cewa shi ne Messi na kasar Argentina.

A farkon makon da muke ciki jaridar wasanni ta MARCA da ke Spain ta rawaito cewa, Paratesh yana yaudarar matan ne ta hanyar nuna musu cewa shi ne ainahin kaftin din Barcelona kuma shaharerren dan wasan duniya,saboda tsabar kamar da suke yi da shi kamar an tsaga kara, wanda kuma idan aka tabbatar da zargin, to tamkar Paratesh ya aikata laifi ne na fyade ta hanyar yaudara.

Sai dai ta shafinsa na Instagram Messin kasar Iran ya musanta zargin tare da shan alwashin garzayawa kotu domin kwatar masa hakkinsa, dangane da bata masa suna da aka yi.

Exit mobile version