Gwamna Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bai wa ‘ya’yan marigayi Sheikh Goni Aisami, malamin addinin Musulunci da aka kashe a jihar takardar daukar aiki su biyu.
Idan ba a manta LEADERSHIP Hausa, ta ruwaito cewa wasu sojoji biyu sun harbe Aisami a ranar Juma’a a Jaji-Maji da ke karamar hukumar Karasuwa a jihar.
- Babu Wanda Ya Bata Wa Wike Rai – Sule Lamido
- Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba – KwankwasoÂ
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce an kama sojojin da suka yi yunkurin sace motar marigayin kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Buni ya bayar da wannan takardun daukar aiki ne a Damaturu lokacin da ‘yan uwan ​​marigayin suka ziyarce shi domin nuna jin dadinsu da goyon bayan da ya basu.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike kan halin da ake ciki dangane da rasuwar malamin.
Gwamnan ya yi alkawarin bayar da tallafi ga iyalan mamacin.
A madadin ‘yan uwa, Ibrahim Aisami, ya bayyana jin dadinsa da sakon ta’aziyya da ziyarar da wata babbar tawagar gwamnati ta kai wa iyalan.
Ya ce aikin da za a bai wa ‘ya’yan zai magance wahalhalun da iyali ke fuskanta, bayan rasuwar malamin.