Maigida Ran Gida: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Don Hana Matasa Aikata Ayyukan Assha

Daga Sabo Ahmad,

Sanin muhimmancin haka ne ya sa  a wannan makon kuma na ga ya dace a kalli matakan da za a dauka na hana matasa aikata assha.

Hakan ce ta sa aka yi hira da Magidanta uku, wadanda suka bayar da shawarwarinsu, kan matakan da suke ganin sun dace a dauka. Dalili shi ne kaucewa aukuwar irin al’amarin da ba kowa ba ne zai ji dadin hakan ba.

Da farko Muhammad Mubarak Jalo Danmalikin Hausawan Mararaba, cewa ya yi, baban matakan da Maigida ko Uba a matsayinsa na shugabanin gidan ya dace su dauka shi ne, tashin farko dai akwai makaranta, sai kula da tarbiyyarsu.

Dabararsa ‘ya’ya makaranta da koyon sana’a hakan zai sa cikin ikon Allah ba su da wani lokacin da har wani abin da zai ja hankalinsu, wajen aikata assha.

Lokaci zuwa lokaci mutum a matsayinsa na Maigida ma fi dacewa ne ya rika zaunar da Matarsa yana fada mata yadda ita ma za ta rika sa ido kan ‘ya’yansu.

Bugu da kari kuma ya rika samun lokaci yana tattaunawa da ‘ya’yansa domin sanin, ko akwai wani taimakon da suke bukata daga gare shi.

Shi kuwa Yahaya Muhammed Ali mai harkar kasuwanci a kasuwar Wuse Abuja cewa ya yi, har ila yau yana yin sharhi kan al’amuran yau da kullun. Cewa ya yi maganar gaskiya ita ce wadda aka saba yi kowace rana ko ina aka ga matashi ya shiga al’amuran da suka shafi ta’addanci, to baya da aikin ko sana’ar yi abin da ya sa haka ke nan. Domin babu wanda za a ce idan ya tafi gurin aikinsa ko sana’arsa a ce kullun zai samu Naira dubu biyu, to wannan babu yadda za a yi ya aikata ta’addanci.

Daga karshe Haruna Umar Talban Mararaba shi a nashi ganin duk Maigida da kwai irin tarbiyyar da yake gabatarwa a gidansa, sai dai kuma tarbiyyyar da ta dace a fara ba yaro ita, ita ce ya tashi da sha’awar neman ilmi wannan kuma ko na addini da kuma na zamani.

Da akwai maganar ciyar da shayar da su ‘ya’yan da Allah ya ba mutum, domin kuwa idan ba haka babu yadda za a yi karatun da ake koya masu ya zauna masu a ka.

Abokai ma suna daga cikin wadanda suke taimakawa wajen wasu suke lalacewa, su shiga aikata ayyukan da ba su dace ba, tuna bin yana karami har ya kasance babba. Shi yasa akwai bukatar mahaifi ya sa ido domin gane ko da su wanene ‘ya’yansa suke yin hulda tare, saboda ta haka ne kafin ya san abinda ake ciki sai har al’amura sun kai ga lalacewa gaba daya daga baya a rika yin dana-sani. Wani lokacin idan ba sa’a ce aka yi ba  wajen samun maganin al’amari, sai abin har ya kai ga cutar da shi matashin, mahaifansa da al’umma kuma a wani lokacin.

Exit mobile version