An sami rahotannin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sayi sabon jirgin shugaban ƙasa ba tare da amincewar Majalisar Ƙasa ba. A cewar binciken jaridar Daily Trust, an sayi sabon jirgin Airbus A330 daga wani babban bankin Jamus bayan da aka kwace shi daga wani Yariman ƙasar Larabawa da ya kasa biyan bashinsa.
Majalisar ƙasa bata tabbatar da samun wata buƙata daga fadar shugaban ƙasa dangane da sayan jirgin ba, inda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana a baya cewa ba a gabatar da irin wannan buƙatar ba. Sai dai ya ce idan har an gabatar da buƙatar, za a yi nazari a kanta idan tana da alaƙa da tsaron ƙasa da jin daɗin al’ummar Nijeriya.
- Manoma Sun Nemi Tinubu Ya Kara Yawan Tallafin Noma
- Shugaba Tinubu Ya Amince A Sake Gina Gadar Wagga Da Ta Rushe
Wani saɓani ya ƙara bayyana lokacin da wata kotun Faransa ta umarci a kwace jirage uku na Nijeriya yayin wata taƙaddama ta doka tsakanin wani kamfanin Sin da gwamnatin jihar Ogun. An ce kamfanin Sin ɗin ya saki jirgin Airbus A330 domin bai wa Shugaba Tinubu damar halartar taro da Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron.
Ko da yake babu wani bayani na cikakken yadda aka sayi jirgin, wasu majiyoyi sun ce za a iya sayen shi ne da kuɗin umarnin kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa wanda ba lallai sai an nemi izinin majalisa ba.
Ƴan majalisar Dattijai da ta Wakilai sun bayyana mamaki kan wannan cefane, suna masu cewa ba a sanar da su komai game da yarjejeniyar ba. Amma majiyoyin gwamnati sun yi nuni da cewa lamarin na iya kasancewa cikin tanade-tanaden kasafin kuɗin da ba a bayyana su ba.
Lokacin da aka tuntubi wakilan fadar shugaban ƙasa da ma’aikatar tsaro, ba su bayar da wata amsa ba. Ofishin mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa shi ma ya bayyana cewa ba su da masaniya game da cikakkun bayanai na sayen jirgin.