Majalisar Wakilai ta Tarayya ta umarci hukumar kula da sadarwa a Nijeriya (NCC) da ta rufe dukkanin shafukan batsa a lungu da sakona a fadin kasar nan domin dakile aikata ashsha da fasadi.
Majalisar tana son kuma hukumar ta tursasa kamfanonin sadarwa da su rufe irin wadannan shafukan cikin gaggawa ba tare da bata wani lokaci ba.
- Mutane 7 Sun Mutu, Kadarorin Miliyan 50.3 Sun Salwanta Dalilin Gobara A Kano
- Manchester United Ta Kai Zagayen Gaba Na Gasar Europa League
Dan majalisa daga Jihar Kwara, Dalhatu Tafoki (APC), shi ne ya dauki nauyin gabatar da kudirin a zauren majalisar dokokin kasar nan.
Da yake jagorantar muhawara kan kudirin, Tafoki ya ce, lamarin shafukan batsa ya zama babban matsala da ake fama da shi a duniyance, ya kara da cewa kwata-kwata Nijeriya ba ta dauki wani mataki na dakile matsalar ba.
A cewarsa, Nijeriya kasa ce mai cike da addini, wadanda mafi yawan addinan da suke akwai suke yaki da irin wannan yada abubuwa na nuna tsiraici da batsa wanda suka kasance haramun a addinance.
Dan majalisar ya zurfafa da cewa kasashe da dama a yankin Asiya, Afrika da Gabas ta Tsakiya sun kafa dokokin da suka haramta yada abubuwan da suka shafi batsa a kasashensu.
Domin tabbatar da kudirinsa, dan majalisar Katsina ya yi tsokaci kan gargadin da masana ilimin halayyar Dan’adam da ilimin zamantakewa suka yi game da mummunan tasirin batsa ga al’umma.
A cewarsa, kallon batsa na iya janyo mutane zuwa ga tafka zina, karuwanci, da sauran ababen lalata.
“Kwararrun masana ilimin halayyar Dan’adam da na ilimin zamantakewa a fadin duniya sun gabatar da gargadi kan kallon batsa, wanda ke kaiwa ga aikata manyan badala,” ya shaida.
Kakakin Majalisar Dokoki na tarayya, Tajudeen Abbas, ya nemi mambobin majalisar da su tafka muhawara kan neman amincewa, inda kuma ‘yan majalisun sun amince da kudirin.
Majalisar ta umarci NCC da ta kakaba tara ga dukkanin kamfanin sadarwar da ya ki bin umarnin da aka bayar na toshe shafukan yanar na batsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp