A ranar Talata ne majalisar wakilai ta kuduri aniyar gudanar da cikakken bincike kan musabbabin ta’addanci da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, musamman yadda ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
An cimma matsayar ne biyo bayan amincewa da kudirin da Hon. Kabiru Mai-Palace, wanda ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun tabarbarewar rashin tsaro a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.
- Manoman Kenya Na Kara Rungumar Fasahohin Inganta Noma Na Sin
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Kama Kwale-kwale Da Muggan Kwayoyin Miliyan N200 A Legas
A muhawarar da ya jagoranta, Hon. Kabiru ya yi tir da karuwar tashe-tashen hankula da ‘yan bindiga ke yi a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, inda ya kai ga sace dalibai mata na jami’ar tarayya da ke Jihar Zamfara da kuma yin garkuwa da wasu masu yi wa kasa hidima (NYSC) lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Sakkwato.
Ya kuma ambaci wasu abubuwan da suka faru na cin zarafin ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba a jihohi daban-daban na yankin.
Bisa damuwa da wadannan abubuwan, Hon. Kabiru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar an sako duk wadanda aka sace tare da kama masu garkuwan domin hukunta su.
Ya kuma bukaci gwamnati da ta tura karin jami’an tsaro a wuraren da ake fama da tashin hankali a yankin.
A nasa martanin, Hon. Ismail Haruna ya bayar da shawarar yin gyaran fuska na sanya sassan yankin Arewa maso gabas, musamman Jihar Bauchi cikin addu’o’i.
A bangarensa, Hon. Suleiman Gummi ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a yaki da ‘yan fashi da makami a yankin Arewa maso yamma.
Ya yi kira ga majalisar da ta bai wa mashawarcin shugaban kasa kan sha’annin tsaro shawara kan shirya taro na musamman domin tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki sun hada kai wajen magance matsalar ‘yan bindiga da kuma rashin tsaro a yankin.
Shi ma da yake jawabi, Hon. Abdullahi Balarabe ya jaddada bukatar tabbatar da shigar da ‘yan kasar cikin tsare-tsaren magance matsalolin ‘yan bindiga da kuma na rashin tsaro da suka addabi yankin Arewa.
A nasa gudunmawar, Hon. Isa Mohammed ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma da gwamnatin da ta gabata.
A ci gaba da kokarin da ake yi na samar da dawwamammen maslaha kan kalubalen tsaro da ake fuskanta, ya bukaci a gudanar da bincike kan ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankin, wanda a cewarsa shi ne ke haifar da karuwar rashin tsaro a Arewa.
Yayin da yake bayyana ra’ayinsa, Hon. Bello Kaoje ya jaddada wajabcin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin ta’adda da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, musamman nazarin alakarsu da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Don haka, majalisar ta umarci kwamitocin hadin gwiwa kan harkokin tsaro da su tabbatar da daukar mataki na gaba.
A yayin zaman, mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu ya bayar da umarnin rufe dukkanin kwamitocin wucin gadi na majalisar domin samar da dama ga kwamitoci na dindindin don gudanar da ayyukansu na doka.
An umurci shugabannin kwamitocin wucin gadi da su gabatar da rahotonsu, sannan kwamitocin majalisa su ci gaba daga inda suka tsaya.