A ranar Talata Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na tura sojojin Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin a matsayin wani ɓangare na aikin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin da nufin kare mulkin dimokuraɗiyya a Yammacin Afirka.
Amincewar ta biyo bayan karanta wata wasiƙar shugaban ƙasa a hukumance inda Shugaban ya nemi amincewar Majalisar Dattawa na ba da izinin tura sojoji zuwa ƙasar da ke maƙwabtaka da ita don hana juyin mulki da kuma hana wargaza cibiyoyin dimokuraɗiyya.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto ’Yan Kasuwa A Sakkwato
- 2027: Ganduje Ya Gargaɗi Mambobin APC Kan Fara Tallata Masu Neman Takarar Gwamna Da Wuri
Bayan gabatar da wasiƙar, Majalisar Dattawa ta yanke shawarar mika kudurin ga Kwamitin bai-ɗaya na majalisar don yin shawarwari kan buƙatar Shugaban.
Nan take, aka amince da ƙudurin bayan Shugaban Majalisar Dattawa ya yi kira da a kaɗa ƙuri’a, inda mafi yawancin ‘yan majalisar dattawan suka amince.














