Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓar bashin sama da dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, domin aiwatar da ayyuka a shekarar 2025 zuwa 2026.
Wannan amincewa ta biyo bayan rahoton kwamitin majalisar da ke kula da batun bashin cikin gida da na waje, wanda Sanata Aliyu Wamakko ya gabatar.
- Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno
- Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Muhimmin Taron NEC
Bayan haka, ana kuma shirin tara dala biliyan biyu daga cikin gida.
Shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gina ababen more rayuwa, noma, tsaro, lantarki da kuma fasahar sadarwa.
An ware dala biliyan uku daga cikin bashin domin gyaran layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.
Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan buƙata.
Sun bayyana cewa hakan ya shafi dukkanin yankunan ƙasar nan kuma yana daidai da yadda sauran ƙasashe ke gudanar da ci gaban tattalin arziƙi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp