Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce a mako mai zuwa ne majalisar za ta tantance sunayen ministoci bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa zauren majalisar domin tantance su.
Lawan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, gabanin dage zaman majalisar.
- Buhari Ya Bukaci ‘Yan Majalisa Da Su Tabbatar Da Sabbin Sunayen Ministoci Da Ya Aike
- An Fafata Da Lawan A Zaben Fidda Gwanin Sanatocin Yobe – Shugaban APC
“Za a tantance wadanda aka nada a matsayin ministoci ranar Laraba, mako mai zuwa”, in ji Lawan.
Shugaba Buhari, a wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuni, 2022, ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da tantance sunayen ministoci bakwai.
Ya ce an gabatar da bukatar tabbatar da sashe na 147(2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 kamar yadda aka gyara.
Wadanda aka nada domin tantancewa sun hada da: Henry Ikechukwu Ikoh – Jihar Abia; Umana Okon Umana – Jihar Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama- Jihar Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah – Jihar Imo.
Sauran sun hada da Umar Ibrahim El-Yakub – Jihar Kano; Ademola Adewole Adegoroye – Jihar Ondo; da Odum Udi – Jihar Ribas.
Hakazalika, Majalisar Dattawa a jiya ta tabbatar da nadin Dr. Hale Gabriel Longpet (Plateau) a matsayin Kwamishinan Zabe na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Tabbatar da Longpet ya biyo bayan la’akari da rahoton kwamitin da ke kan al’amuran zabe.
Shugaban kwamitin, Sanata Kabiru Gaya (Kano ta Kudu), a jawabinsa, ya ce an gabatar da nadin Longpet ne bisa tanadin sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya, 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima).
Ya bayyana cewa wanda aka zaba a lokacin da ya gurfana gaban kwamitin domin tantancewa, ya bayar da bayani dangane da rayuwarsa, kwarewar aikinsa, dacewarsa, cancantarsa ​​da amincinsa na nadinsa a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Ya ce mambobin Kwamitin sun yaba da kyakkyawan tsarin Karatu da kuma gamsassun amsoshi ga tambayoyin da aka gabatar.
Bayan haka, an tabbatar da wanda aka zaba a
zauren.