Mataimakin wakiliyar mata a Majalisar dinkin duniya, Lansana Wonneh ya koka kan yadda mata manoma da ke a karkara a kasar nan, ba samun tallafin a kan Sana’ar ta su ta yin noma.
Ya sanar da cewa, matan manoma a karkara, na bayar da gagarumar gudunmawa,musamman wajen kara bunkasa samar da abinci da kuma kara habaka tattalin arzikin kasar nan.
Ya sanar da hakan ne a wani taro a garin Kalaba a kan bikin zagayowar ranar mata manoma da ke a karkara ta duniya, inda ya ci gaba da cewa, an shirya taron ne domin a kara wa matan manoma karkashin kokarin da suke yi na samar da wadataccen abinci, musamman mai gina jiki a daukacin fadin Nijeriya.
Wonneh ya ce an shirya taron ne domin zaburar da mata mazauna karkarar da ke kokarin samarwa, da sarrafawa, hadi da tattata abinci don ciyar da al’umma, duk da watsi da su da ake yi a kasar.
Ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta hada kai da Gwamnatin Nijeriya domin kawo gyara a lamarin.
“An shirya taron ne domin a kara wa matan manoma karkashin kokarin da suke yi na samar da wadataccen abinci, musamman mai gina jiki a daukacin fadin Nijeriya da kumakara karfafa masu gwiwa don su kara samar wa da kawunan su da kudaden shiga don sana’ar ta su ta kara bunkasa”.
A cewar Wonneh ya zama wajibi matan manoman da ke a karkara a dinga tallafa mUsu, musamman idan aka yi dubi da irin wahalhalun da suke fuskanta a lokacin gudanar da aikin na su na noman.
Ya sanar da cewa, burin da majalisar ta ke da shi a kan matan manoman na karkara shine, aga suna samun kayan aikin noman, musamman na zamani da kuma samar masu da wadatattun kudade.
Ya yi nuni da cewa, tallafin zai taimaka masu matuka wajen kara mayar da hankali a kan gudanar da aikin na su na noman.
A wata sabuwa kuwa, an ankarar da gwamatin tarayya kan mahimmancin da ke tattare da san ya mata manoma a daukacin fadin kasar nan a cikin shirye-shiyen aikin noma na kasar.
Wannan ankararwar ta fito ne daga bakin Hajiya Amina Jibrin ita ce, shugabar kungiyar mata manoma kanana da da ke a kasar nan.
A Jawabin da ta yi a kwanan baya a bikin ranar abinci ta duniya Hajiya Amina Jibrin ta bukaci da a tallafa wa manoman, musamman idana aka yi dubi da yadda iftila’in ambaliyar ruwan sama ta yiwa wasu manoman kasar nan barna a gonakansu, inda ta sanar da cewa, matan manoma musamman na bukatar tallafi domin su samu samar ci gaba da yin noman da kuma tsyawa da kafafunsu.
Shugabar ta ci gaba da cewa, ya zama wajibi mahukunta a kasar nan da su samar da dokokin da za su bayar da damar tallafa wa kananan manoma, musamman a dora su a kan yin inshorar aikin noma.
Hajiya Amina ta kuma shawarci gwamnatin jihar Bauchi ta kebe kanana manoman da ke a fadin jihar, bisa yarjejeniyar da aka sa wa hannu ta Maputo.