Majalisar Dokokin Bauchi Ta Kada Kuri’ar Rashin Gamsuwa Da Kwamishinan Ilimin Jihar

Daga Khalid Idris Doya,

Majalisar Dokoki ta jihar Bauchi a yau Litinin ta kada kuri’ar rashin gamsuwa da kwamishinan Ilimi na jihar Dakta Aliyu Tilde bisa abun da ta kira rashin ladabi da biyayya ga mambobin majalisar.

A bisa muhimmanci harkar ilimi Majalisar ta gudanar da zama na musamman a karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Rt. Hon. Abubakar Yakubu Suleiman inda suka cimma matsayar janye tabbatarwa tare da sahale kwamishinan da suka yi a cikin mambobin Majalisar zartaswa na jihar.

Majalisar ta ce ta aike da gayyata wa kwamishinan na ya bayyana a gabanta domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa da karfe 10 na safiya amma bisa rashin mutuntasu bai zo kwaryar Majalisar ba har zuwa karfe 1 na rana.

Majalisar wacce a halin yanzu take cigaba da amsar kariya kan kasafin kudin 2022 daga ma’aikatun da rassan gwamnati, bayan wannan matakin, Majalisar ta bukaci babban sakataren dindindin na ma’aikatar ilimin da ya cigaba da kare kasafin kudin ma’aikatar a gaban Majalisar dokoki ta jihar tare da jingine Tilde a gefe.

Wannan matakin na zuwa bayan kudirin da shugaban kwamitin ilimi na majalisar Hon. Babayo Muhammad mai wakiltar mazabar Hardawa ya gabatar.

Dan majalisar ya shaida a gaban Majalisar cewa Kwamishinan na ilimi ya nuna dabi’ar rashin mutuntawa ga mambobin majalisar lokacin da yake kare kasafin kudin ma’aikatarsa.

Ya kara da cewa, Tilden ya musu tambaya ta rashin girmamawa a lokacin da ya zo gabansu inda ya kama tambayarsu ko su waye “alhali ya riga ya san ko mu su waye”.

Bayan dai rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu ne suka nemi ya tashi ya yi tafiyarsa tun da ban gane da su wa yake tare ba.

Don haka Majalisar ta cimma matsayar cewa babban sakataren ma’aikatar ilimin zai cigaba da kare kasafin, tare da janye tantancewar Dakta Aliyu Usman Tilde a matsayin Kwamishinan Ilimi na jihar Wanda Majalisar ta yi a ranar 17 ga watan Agustan 2021.

Da aka tuntubi Tilde kan wannan batun ya bayyana cewar zai yi cikakken bayani kan lamarin zuwa gobe.

Exit mobile version