Majalisar dokokin jihar Kaduna ta karbe ragamar ayyukan majalisar hukumar Kagarko sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.
Haka kuma, ‘yan majalisar sun dakatar da kansiloli takwas daga karamar hukumar har sai baba-ta-gani.
- Ruɗani A Kan Shari’ar Abba Da Gawuna: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar NNPP A Rubuce
- Gwamnatin Tarayya Ta Soke Lasisin Ma’adinai 1,633
Kansiloli takwas da abin ya shafa sun hada da Danjuma Padalo, unguwar Iddah; Adamu Abdulaziz, Kagarko ta kudu; Livinus Makama, unguwar Aribi; da Samson Hazo, unguwar Katugal.
Sauran sun hada da, Amos Egoh, Unguwar Kushe; Idris Abubakar, Jere ta arewa; Zakaria Musa, unguwar Kukui; da Rabo Musa, unguwar Kurmin Jibrin.
Wasu majiyoyi na kusa da Majalisar da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce, dakatarwar nasu bata rasa nasaba da tsige Shugaban karamar hukumar, Nasara Rabo ba bisa ka’ida ba, ba tare da bin ka’ida ba da kansilolin suka yi.