Majalisar Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta bayyana shirin fara amfani da Fasahar AI na Wucin-Gadi (AI) domin inganta tasiri da inganta ayyukan dokoki a majalisar. Shugabar majalisar, Rt. Hon. Memounatou Ibrahima, ta sanar da haka a lokacin rufe taron bita na majalisar karo na biyu a 2025 da aka gudanar a birnin Fatakwal na Jihar Rivers, wanda taken sa shi ne: “Amfani da Fasahar AI Don Inganta Ayyukan Majalisa, Gwamnatin Da Cigaba a Yankin ECOWAS.”
Taron ya ɗauki kwanaki uku, inda masana suka gabatar da bayanai, aka gudanar da tattaunawa da mahawara kan muhimmancin wannan fasaha wajen tallafa wa ayyukan dokoki. An kuma jaddada buƙatar samar da ƙa’idojin da za su kare yankin daga haɗarin AI, musamman ganin ƙalubalen da ke tattare da ƙarancin ababen more rayuwa a Afrika ta Yamma.
- ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000
- ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000
A jawabin da aka karanta a madadin shugabar, ta hannun mataimakinta na huɗu Billay Tunkara, an bayyana AI a matsayin “sauyin da ba za a iya samun ci gaba ba tare da shi ba”, inda aka ce cikin ƙanƙanin lokaci fasahar ta riga ta sauya tsarin tattalin arziƙi, da zamantakewa da mulki a yankin. Shugabar ta jaddada cewa idan aka sarrafa fasahar yadda ya kamata, za ta taimaka wajen samar da ingantattun dokoki, da tattaunawa mai ma’ana da kuma ƙarfafa ikon sa ido na majalisa.
Sai dai wasu ƴan majalisa sun nuna damuwa cewa fasahar na iya kawo barazana idan ba a yi amfani da ita yadda ya kamata ba. Duk da haka, an yi kira da a yi amfani da AI ta yadda za a ci gajiyar damar da take bayarwa ba tare da barin ta lalata ƙimomin ɗan Adam da tushen dimokuraɗiyya ba.
Taron bitar ya zama wani sabon mataki na haɗin gwuiwa a tsakanin ƙasashen ECOWAS don shigar da AI cikin ayyukan majalisa. A cewar shugabar, shawarwarin da aka tattara za su zama tubalin tsare-tsaren da za su tabbatar da cewa majalisar ta rungumi wannan sabuwar fasaha cikin nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp