Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da ɗaukar sabbin malaman makaranta dubu ɗaya wadda hukumar bada ilimin bai ɗaya ta jiha (SUBEB) ta kammala.
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a yayin zamanta wadda ta gabatar a ranar talatar makon da ya gabata a birnin na Dutse.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da ɗan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Kazaure Alhaji Bala Hamza Gada ya gabatar gaban majalisar kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Bulangu Alhaji Muhammad Abdullahi Bulangu ya marawa baya a ya yin zaman.
Haka kuma ta umarci Hukumar ta dakatar da duk wani lamari da ya shafi ɗaukar malaman, har sai Kwamatin ta ya kammala binciken sa tareda gabatar da sakamakon binciken gaban majalisar.
Waɗannan ‘yan majalisu biyu sun bayyana cewa wannan ƙuduri nasu da suka gabatar gaban majalisar, ya biyo bayan samun korafe korafe daga kananan hukumomi da dama akan yadda daukar malaman makarantar.