Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara yawan kudaden da take warewa shirin (EGF) na Hukumar fitar da kaya zuwa ketare (NEPC).
Dan Majalisa Mukhtar Zakari Chawai ya gabatar da wannan bukatar a zaman da Majalisar ta yi a ranar Alhamis.
- Bai Kamata Kungiyar EU Ta Biyewa Masu Burin Rusha Alakarta Da Sin Ba
- Sokoto Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 15 Ga Gyaran Makarantu, Motocin Alkalai Da SauransuÂ
Mukhtar ya sanar da Majalisar cewa, shirin wanda Hukumar ta NEPC ke sanya ido akai, manufarsa shi ne, a taimakawa wajen kayan da ake sarrafa a kasar nan ake kuma fitar da su zuwa kasashen waje.
Kazalika, shirin na kuma taimakawa wajen samar da tallafin kudade ga fannin kayan da ba su shafi fannin mai ba, wadanda kuma ake fitar da su zuwa ketare.
A cewar Dan Majalisar, irin wannan daukin na kudaden na taimakawa kamfanonin kasar da kuma samun damar samun rancen kudade daga gun Gwamnati da sauransu.
Bugu da kari, samar da daukin kudaden domin hada-hadar kasuwanci a kasar nan, abu ne da aka damu da shi matuka, duba da yadda Gwamnatin kasar, ba ta bayar da wadatattun kudaden da suka kamata.
Kazalika, hada-hadar kasuwanci a kasar nan da dama, an daktar da su, saboda rashin samar da kyakyawan tsare-tsaren kasuwanci a kasar.