Majalisar Wakilai ta dakatar da Babban Bankin Nijeriya (CBN), daga sallamar ma’aikata 1,000 da yake shirin yi.
Ta kafa kwamiti na musamman domin bincike kan lamarin, tare da duba yadda za a bi ka’idoji wajen biyan ma’aikatan hakkokinsu da ya kai Naira biliyan 50.
- An Gudanar Da Taron Gabatar Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Ciniki Cikin ‘Yanci Ta Hainan
- Kiyaye Rayukan Al’umma: Majalisa Na Shirin Keɓe Wa Masu Sayar Da Iskar Gas Wuri A Wajen Birnin Kano
Dan majalisa Inuwa Garba, ya bayyana cewa majalisar na da hakkin sa ido kan irin wannan lamari, don tabbatar da adalci.
Shi ma masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu, ya ce ba daidai ba ne a sallami mutane da yawa ba tare da bin tsari ba, musamman a wannan yanayi na tattalin arziki.
Masu sharhi sun yaba da matakin na majalisar, inda suke ganin hakan zai taimaka wajen kare hakkin ma’aikata da kuma bin doka cikin tsarin gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp