Majalisar wakilai ta bayyana cewa, Nijeriya tana tafka asarar dala miliyan 750 a bangaren gas a duk shekara. Haka kuma, ta nuna damuwarta da fashewar gas lokacin da ake amfani da shi wajen samar da wutar lantarki a cikin kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, tana kokarin kawo karshen fashewar gas kafin shekarar 2025. A cewar gwamnatin tarayya, kawo karshen fashewar gas zai sa kasar nan ta samu damar amfanan tattalin arziki daga bangaren gas bisa yarjejeniyar da ta shirya da kamfanin makamashi da ke Paris.
Hadakar kwamitin majalisa ta fannin albarkatun gas da makamashi ya gudanar da sauraron jin ra’ayin mutane a kan kawo karshen fashewar gas a cikin kasar nan a ranar Litinin. Shugaban kwamitin, Nicholas Mutu ya bayyana cewa, bincike ya nuna cewa kasar nan tana tafka asarar dala miliyan 750 a duk shekara daga fashewar gas.
Mutu ya ce, “dole ne mu hada hannu da karfe wajen dakile matsalar fashewar gas domin yana lalata muhallin da tattalin arzikin mutanen yankin Neja Delta da ke raguwar kudader masu yawa ga gwamnatin tarayya.
“Bincike ya nuna cewa, a duk shekara, Nijeriya tana tafka asarar dala miliyan 750 daga cikin harajin bangaren gas.”
A shekarar 2018, gwamnatin tarayya ta kashe dala miliyan biyu a bangaren gas wanda akwai bukatar dakile wannan matsala cikin gaggawa.
Ministan albarkatun mai, Timipre Sylba ya bayyana cewa, fashewar gas yana bukatar daukan matakin gaggawa musamman ma a dai-dai wannan lokaci da aka kulla yarjejeniya. Sylba ya kara da cewa, kasar nan ta samu nasarar rage fashewar gas wanda ya kai kashi takwas.
Ya ce, “ma’aikatan mai ta kasa ta gudanar da shirin fadada albarkatun mai a shekarar 2020.
“A farkon wannan shekara, mun lissafa shekarar 2021 a matsayin shirin samar da gas na tsawan shekaru 10, muna tsammanin cimma wannan buri a shekarar 2025.”
Minista ya bayyana cewa, shekarar 2020 an samu matsaloli masu yawa. Ya ci gaba da cewa, ma’aikatarsa ta gudanar da wani shiri kan gas a watan Disambar shekarar 2020, wannan ta yi kokarin kawo karshen fashewar gas a cikin kasar nan.
Haka kuma, shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC), Mele Kyari ya bayyana hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar fashewar domin bunkasa tattalin arziki. Ya bayyana cewa, bayan an samu nasarar dakile wannan matsala za a bunkasa tattalin arziki.
Ministan muhalli, Dakta Muhammed Abubakar wanda ya samu wakilcin Daraktar muhalli, Abbah Suleman ya bayyana cewa, fashewar gas yana matukar lalata muhalli.
Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin shari’a, Onofiok Luke ya bukaci a kawo karshen fashewar gas.